Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana kafa ginshiƙin mai ƙarfi domin samun cigaba mai ɗorewa tare kuma da bunƙasar tattalin arziki ga kowa, ta hanyar ɗaukar tsauraran matakai.
Idris ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin membobin ƙungiyar fafutikar sake zaɓen Tinubu mai suna ‘Grassroots Advocacy for Tinubu (GAT) 2027’, waɗanda suka kai masa ziyarar ban-girma.
A cewar ministan, gwamnatin ta ɗauki wasu matakai masu tsauri amma masu muhimmanci domin daidaita tattalin arzikin ƙasar nan, inda ya bayyana cewa tuni alamun farfaɗowa suka fara bayyana a sassa daban-daban na tattalin arziki.
Ya ce: “An ɗauki waɗannan matakai ne domin daidaita tattalin arziki da maido da ƙwarin gwiwa. Abin da muke gani a yau shi ne ginshiƙin cigaba mai ɗorewa da kuma wadata da za ta amfani kowa.”
Ya jaddada cewa dole ne a kare kyakkyawan yanayin tattalin arzikin da Nijeriya ke ciki ta hanyar haɗin kai, yaɗa labarai cikin gaskiya, da kuma goyon bayan manufofin gwamnati baki ɗaya.
Ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya ko ɓata sunan ƙasa yana iya karya gwiwar masu zuba jari tare da daƙile cigaba.
“Dole ne mu faɗi alheri kuma mu faɗi gaskiya game da Nijeriya,” inji shi. “Idan muka nuna daidaito da haɗin kai, za mu jawo hankalin masu zuba jari sannan mu samar wa mutanen mu damarmaki.”
Idris ya yaba wa ‘ya’yan ƙungiyar GAT bisa jajircewar su wajen wayar da kan jama’a, inda ya kuma amince da shawarar ƙungiyar na yin haɗin gwiwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai wajen faɗakar da jama’a, jawo matasa a jiki, da kuma kyakkyawan tsarin yaɗa labarai.
Ya sake jaddada ƙudirin Shugaban Ƙasa Tinubu na gina Nijeriyar da za ta amfani kowa, ba tare da la’akari da addini ko yanki ba, yana mai cewa haɗin kan ƙasa shi ne jigon hangen nesa na wannan gwamnati.
Shi ma a nasa jawabin, jigo a ƙungiyar GAT, Farfesa Ochugudu Achoda Ipuele, ya ce sun kai ziyarar ne domin yi wa ministan bayani kan ayyukan ƙungiyar da kuma nuna goyon baya ga aikin sa na sanar da ’yan Nijeriya gaskiyar manufofin gwamnati.
Ya ce: “Mun zo nan ne don mu taya ku murnar wannan babban nauyi da kuke ɗauke da shi ga Nijeriya, wanda shi ne sanar da ƙasa, fito da manufofin gwamnati fili, da kuma kai sahihan bayanai zuwa ga talakawa.”
Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta himmatu wajen kare manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta hanyar ƙalubalantar labaran ƙarya, musamman a lokutan zaɓe, da kuma jawo matasa a jiki.
Farfesa Ipuele ya ce: “Wannan ƙungiya a shirye take ta mayar da martani nan take kan duk wani labarin ƙarya, tare da haɗa kai da matasa, domin ganin cewa yayin da muke tunkarar shekarar 2027, Shirin Sabunta Fata ya ci gaba tare da samar da ƙarin shirye-shirye ga ƙasa.”







