Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a yau Laraba, ta ba da beli ga Alhaji Abubakar Malami, SAN, tsohon Ministan Shari’a Kuma Babban Lauyan Ƙasa (AGF); da ɗan sa, Abubakar Abdul’aziz, da matar sa, Hajiya Asabe Bashir, kan kuɗin beli na naira miliyan 500 kowannen su, tare da masu tsaya musu guda biyu kowanne a irin wannan adadi.
Mai Shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin sa, ya bayyana cewa dalilan da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Kuɗi (EFCC) ta gabatar domin hana bayar da beli ba su da ƙarfi da gamsasshiyar hujja da za su hana waɗanda ake ƙarar samun belin.
A cewar sa, hujjojin sun fi karkata ne zuwa zato da hasashe.
Saboda haka, alƙalin ya amince da belin su kan kuɗin naira miliyan 500 kowannen su, tare da masu tsaya masu guda biyu waɗanda dole ne su kasance masu mallakar kadarori a Asokoro, Maitama ko Gwarimpa, a cikin Babban Birnin Tarayya (FCT).
Ya ce dole ne a tantance takardun mallakar kadarorin ƙasa ta hannun mataimakin magatakardan kotu mai kula da shari’o’i.
Har ila yau, ya ce dole ne waɗanda ake ƙarar su miƙa dukkan fasfofin tafiyar su na ƙasashen waje ga mataimakin magatakardan kotu mai kula da shari’o’i, kuma ba za su yi tafiya zuwa wata ƙasa ba sai da izinin kotu.
Mai Shari’a Nwite ya kuma ba da umurnin cewa waɗanda ake ƙara da masu tsaya masu su miƙa hotunan fasfo guda biyu-biyu ga magatakardan kotu.
Bugu da ƙari, alƙalin ya ba da umurnin cewa a tantance wuraren zamantakewar masu tsaya masu ɗin ta hannun magatakardan kotu.
Mai Shari’a Nwite, wanda ya umurci cewa dole ne waɗanda ake ƙara su ci gaba da kasancewa a kurkukun Kuje da na Suleja har sai sun cika dukkan sharuɗɗan belin su, ya ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Janairu domin fara sauraron shari’ar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa EFCC, a cikin tuhumar da aka yi wa laƙabi da: FHC/ABJ/CR/700/2025, ta sanya sunan tsohon ministan, Hajiya Asabe Bashir (matar sa), wani ma’aikacin kamfani da ke da alaƙa da tsohon ministan, wato Rahamaniyya Properties Ltd, da kuma ɗan sa, a matsayin waɗanda ake ƙara na farko, na biyu da na uku bi da bi.
EFCC, a cikin tuhume-tuhume guda 16, ta zargi waɗanda ake ƙarar da aikata mu’amaloli masu cike da shakku tare da yunƙurin ɓoye asalin kuɗaɗen da ba su halatta ba na biliyoyin naira ta hanyar asusun banki da sayen kadarori a sassa daban-daban na Abuja, Kano da Kebbi.
Ana zargin sun aikata laifukan ne tsakanin shekarun 2015 da 2025, wani lokaci da ya haɗa da shekaru takwas da Malami ya yi yana aiki a matsayin Ministan Shari’a a zamanin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Hukumar ta zargi cewa Malami, ɗan sa da Asabe sun haɗa baki wajen ɓoye asalin kuɗaɗen, sayen kadarori ta ɓarauniyar hanya, da riƙe kuɗaɗen da ake zargin sun san cewa haramtattun kuɗaɗe ne, abin da ya saɓa wa Dokar Hana da Kare Safarar Kuɗi ta shekarar 2011 (da aka yi wa gyara) da kuma ta 2022.
A tuhuma ta ɗaya, EFCC ta yi zargin cewa tsakanin Yuli 2022 da Yuni 2025, Malami da ɗan sa sun umurci kamfanin Metropolitan Auto Tech Limited da ya ɓoye sama da naira biliyan 1 (N1,014,848,500) a cikin asusun Bankin Sterling, duk da sanin cewa haramtattun kuɗaɗe ne.
Tuhuma ta biyu ta bayyana cewa tsakanin Satumba 2020 da Fabrairu 2021, su biyun sun ɓoye sama da naira miliyan 600 (N600,013,460.40) ta hanyar wannan kamfani.
A tuhuma ta uku, hukumar ta ce a watan Maris 2021, Malami da ɗan sa sun riƙe naira miliyan 600 a matsayin jinginar kuɗi domin rancen naira miliyan 500 da Bankin Sterling ya bai wa Rayhaan Hotels Ltd, duk da sanin cewa kuɗaɗen ba halastattu ba ne.
Tuhuma ta huɗu ta ce a watan Nuwamba 2022, Malami, ɗan sa da Asabe sun ɓoye naira miliyan 500 da aka yi amfani da su wajen sayen wani katafaren gida mai hawa biyu a Maitama, Abuja.
A tuhuma ta biyar, EFCC ta yi iƙirarin cewa tsakanin Nuwamba 2022 da Satumba 2024, su ukun sun haɗa baki wajen ɓoye naira 1,049,173,926.13 da aka biya ta asusun Bankin Union na Meethaq Hotels Ltd.
Tuhuma ta shida ta zarge su da cewa tsakanin Nuwamba 2022 da Oktoba 2025, Malami da ɗan sa sun karɓi ikon sarrafa naira 1,362,887,872.96 daga wannan asusu, duk da sanin cewa haramtattun kuɗaɗe ne.
Tuhuma ta bakwai ta ce a tsakanin Nuwamba zuwa Disamba 2018, Malami da Asabe sun ɓoye naira miliyan 700 da aka yi amfani da su wajen sayen gida mai lamba 3, Onitsha Crescent, Garki, Abuja (Hamonia Hotels Ltd).
A tuhuma ta takwas, tsakanin Satumba da Disamba 2020, su biyun da Asabe sun ɓoye naira miliyan 850 domin sayen wani fili a yankin Jabi, Abuja (Meethaq Hotels Ltd).
Tuhuma ta tara ta bayyana cewa a Fabrairu 2018, Malami da Hajiya Asabe Bashir sun sayi gida mai lamba 3, Rhine Street, Maitama, Abuja, kan kuɗi naira miliyan 430, wanda ake zargin kuɗaɗen ba halastattu ba ne.
A tuhuma ta goma, an ce su biyun sun ɓoye naira miliyan 210 a Fabrairu 2018 domin sayen wata kadara a yankin Asokoro, Abuja.
Tuhuma ta goma sha ɗaya ta ce tsakanin Maris da Yuni 2021, sun ɓoye naira miliyan 325 da aka yi amfani da su wajen sayen gida mai lamba 1241B, Asokoro District, Abuja.
A tuhuma ta goma sha biyu, EFCC ta yi zargin cewa tsakanin Nuwamba 2015 da Janairu 2016, su biyun sun ɓoye naira miliyan 120 da aka yi amfani da su wajen sayen gida mai lamba 27, Efab Estate, Gwarimpa, Abuja.
Tuhuma ta goma sha uku ta ce a Nuwamba 2022, tsohon Ministan, matar sa da ɗan sa sun haɗa baki wajen ɓoye kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen wani katafaren gida a Amazon Street, Maitama, Abuja.
A tuhuma ta goma sha huɗu, tsakanin Disamba 2016 da Afrilu 2022, Malami, Asabe da wasu sun haɗa baki wajen sayen ƙarin kadarori ga Malami da kuɗaɗen da ake zargin haramtattu ne.
Tuhuma ta goma sha biyar ta ce tsakanin Yuni 2023 da Janairu 2023, Malami ya ɓoye “Naira miliyan 537 da aka yi amfani da su wajen sayen kadarori da dama a Abuja, Kebbi da Kano.”
A tuhuma ta goma sha shida, EFCC ta ce tsakanin Oktoba 2018 da Disamba 2021, Malami ya ɓoye “Naira miliyan 415 da aka yi amfani da su wajen sayen kadarori da dama a Abuja, Kebbi da Kano.”
EFCC ta ce tana shirin kiran shaidu da dama, ciki har da ma’aikatan hukumar, wakilan bankuna, ‘yan canjin kuɗi da sauran ƙwararrun masana harkar kuɗi.
Muhimman shaidu sun haɗa da Folarin Dare, Chinedu Eneanya, Sani Lukeman, Abdulrahman Musa Basheer, Jamilu Mohammed, da wakilan Zenith Bank Plc da Sterling Bank Plc.
Ana sa ran Folarin Dare, Chinedu Eneanya da Sani Lukeman za su bayar da shaida kan yadda EFCC ta samu bayanan sirri da ƙorafe-ƙorafen zargin babbar rashawa kan tsohon ministan.
Abdulrahman Musa Basheer zai gabatar da hujjoji kan rawar da kamfanin Rahamaniyya Properties Ltd ya taka wajen zargin saya wa Malami kadarori.







