• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya amince a ba ƙananan ’yan kasuwa tallafin N250,000 a Katsina

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 21, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tinubu ya amince a ba ƙananan ’yan kasuwa tallafin N250,000 a Katsina
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a wurin ƙaddamar da taro karo na 9 na shirin a Katsina

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a wurin ƙaddamar da taro karo na 9 na shirin a Katsina

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin N250,000 ga ƙananan ‘yan kasuwa da matsakaitan masana’antu (MSME) da suka nuna bajinta a yayin Faɗaɗɗen Taron Ƙanana da Matsakaicin Masana’antu na Ƙasa (Expanded National MSME Clinic) da aka gudanar a Katsina.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shi ne ya bada wannan sanarwar a lokacin ƙaddamar da taro karo na 9 na shirin, wanda aka shirya don tallafa wa ƙanana da matsakaitan sana’o’i da kuma farfaɗo da tattalin arzikin al’umma.

Shettima ya bayyana cewa an samar da shirin ne domin kawo hukumomin gwamnati kusa da masu sana’a da kuma ƙarfafa fasahar ƙirƙire-ƙirƙire, samar da ayyukan yi, da sauƙaƙa samun rajista ko tallafi daga cibiyoyi kamar CAC, NAFDAC, SMEDAN, da Bankin Masana’antu.

Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani ɓangare ne na yunƙurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun naira biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da ‘yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa naira miliyan 5 da kashi tara cikin ɗari a matsayin kuɗin ruwa, da kuma naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaban Ƙasa da ke bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke bada tallafin N50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya a faɗin ƙasar nan.

Haka kuma gwamnatin ta samar da Asusun Tallafin Masana’antu daga Gwamnati (Manufacturers Fund) na naira biliyan 75 don tallafa wa masana’antu wajen rage tsadar samar da kayayyaki da sufuri.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce sama da ’yan kasuwa 39,000 a Jihar Katsina sun amfana da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya, inda aka raba naira biliyan 2.5 a matsayin tallafi da rance mai rangwame. A ƙarƙashin shirin RAPID, Shettima ya ce ’yan kasuwa 23 daga yankunan karkara sun samu fiye da naira miliyan 112 don faɗaɗa kasuwancin su.

Ya kuma yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kafa KASEDA, yana mai cewa Katsina na zama cibiyar cigaban masana’antu, noma, da kasuwancin yanar gizo a Arewacin Nijeriya.

Tags: Dikko Umar RaɗɗaKashim ShettimaKatsinatallafi
Previous Post

Tinubu ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa

Next Post

Gwamnatin Tarayya za ta zuba jarin dala miliyan 220 don samar da ayyukan yi — Shettima

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya za ta zuba jarin dala miliyan 220 don samar da ayyukan yi — Shettima

Gwamnatin Tarayya za ta zuba jarin dala miliyan 220 don samar da ayyukan yi — Shettima

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!