• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 22, 2026
in Siyasa
A A
0
Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya waɗanda suka yi nasara a zaɓuɓɓukan da aka gudanar jiya Asabar a Babban Birnin Tarayya (FCT) da jihohin Kano da Ribas murna.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na FCT, tare da zaɓen cike gurbi a mazaɓun Ahoada East II da Khana II na Jihar Ribas, da kuma mazaɓun Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano.

Shugaba Tinubu ya buƙaci waɗanda suka lashe zaɓen da su yi aiki da kyautatawa, kishin ƙasa da kuma sadaukar da kai, yana mai jaddada cewa amanar da al’umma suka ba su wata amana ce mai tsarki da ya wajaba su kiyaye.

Haka kuma, ya yaba wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa irin nasarorin da ya samu a yankin, wanda ya ce sun taimaka wajen samar wa jam’iyyar APC gagarumar nasara a zaɓen.

Shugaban ya kuma taya shugabannin APC na ƙasa da na jihohin Kano da Ribas, tare da dukkan membobin jam’iyyar, murnar nasarorin da aka samu a zaɓen.

Ya yaba wa INEC, jami’an tsaro da masu kaɗa ƙuri’a bisa gudanar da zaɓen cikin lumana da nasara, tare da yaba wa dukkan ‘yan takarar da suka nuna jajircewa da bin doka yayin fafatawar zaɓen.

A cewar sa, nasarar gudanar da zaɓuɓɓukan cikin nasara na ƙara ƙarfafa dimokiraɗiyya a ƙasar nan, yana mai kira ga INEC da ta ci gaba da inganta ayyukan ta domin samar da sahihin tsarin zaɓe a nan gaba.

Tags: FCTINECKanoTinubuzaɓeƘanananHukumomi
Previous Post

Yadda shigar da ‘yan canji cikin kasuwar canjin kuɗi ta NFEM ya ƙara wadatar dala da buɗe hanyar daidaituwar naira

Next Post

Yadda Aka Raba Musulmi Da Ƙur’ani

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

April 28, 2026
A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027
Siyasa

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

April 25, 2026
Next Post

Yadda Aka Raba Musulmi Da Ƙur'ani

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!