• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda shigar da ‘yan canji cikin kasuwar canjin kuɗi ta NFEM ya ƙara wadatar dala da buɗe hanyar daidaituwar naira

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
February 20, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda shigar da ‘yan canji cikin kasuwar canjin kuɗi ta NFEM ya ƙara wadatar dala da buɗe hanyar daidaituwar naira

Matakin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka na ba da lasisi ga masu sana’ar canjin kuɗi, wato ‘Bureau De Change’ (BDC) damar shiga Kasuwar Canjin Kuɗi ta Nijeriya (NFEM) ya haifar da sakamako nan take ga naira, tare da rage giɓin da ke tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan fage.

A makon da ya gabata, CBN ya fitar da wata sanarwa ga Bankunan Dillalan Canji Masu Izini da kuma jama’a game da shiga kasuwar NFEM da aka bai wa BDCs masu lasi.

Manufar matakin ita ce ƙara wadatar dala a ɓangaren ‘yan kasuwa da masu saye kai tsaye, da kuma rage matsin lamba a kasuwar bayan fage.

Tun bayan fitar da sanarwar, giɓin da ke tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage ya ragu sosai, tun ma kafin BDCs su fara samun cikakkiyar damar sayen dala.

Bambancin farashin da ya kai Naira 92 a ranar Laraba ta makon jiya ya ragu zuwa Naira 33 a ranar Litinin.

Wannan giɓin da ya wuce N90 shi ne mafi faɗi tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya ‘yantar da tsarin canjin kuɗi a 2023.

A ranar Litinin, naira ta kai ƙololuwar shekaru biyu a kasuwar hukuma, inda aka sayar da dala kan N1,347.78.

Bayanai daga CBN sun nuna cewa naira ta ƙara ƙarfi da Naira 7.64 idan aka kwatanta da Naira 1,355.42 na ranar Juma’a, wanda ke nuna ƙarin daraja da kashi 0.57%.

A kasuwar bayan fage kuwa, naira ta ƙara ƙarfi zuwa Nara 1,380 kan dala ɗaya bayan ta buɗe ciniki a Naira 1,390.

Wannan ya rage giɓin da ke tsakanin kasuwannin da kashi 2.4%, yayin da Naira ta samu Naira 40 idan aka kwatanta da Naira 1,420 na ranar Juma’a.

Da wannan yardar wadda CBN ya bai wa kowane BDC damar sayen har dala $150,000 a mako, ana kallon matakin a matsayin babbar hanya ta ƙara wadatar dala da tallafa wa daidaituwar naira, musamman ga ‘yan kasuwa da masu buƙatar canjin kuɗi na gaskiya.

Ɓangaren BDC na taka muhimmiyar rawa wajen samar da dala ga ƙananan ‘yan kasuwa da masu buƙatar kuɗin waje.

A cikin ‘yan shekarun nan, CBN ya aiwatar da gyare-gyare da nufin haɗa farashin canji wuri guda, kawar da karkacewa, da ƙara gaskiya a kasuwa. Wannan ya ba kamfanoni damar tsara harkokin su cikin kwanciyar hankali.

Wani muhimmin ɓangare na gyaran shi ne sake ƙarfafa jari da bai wa BDCs 82 lasisi ƙarƙashin sabuwar doka.

Masu lasisi mai daraja ta ɗaya, wato Tier-1 sun tara jarin Naira biliyan 2, yayin da Tier-2 suka tara Naira miliyan 500 duk a matsayin gejin mafi ƙanƙantar jari.

Bisa dokar BOFIA 2020 da ƙa’idojin 2024, CBN ya amince da su tare da bai wa kowannen su damar samun dala kai tsaye daga NFEM.

Sanarwar da Musa Nakorji, daraktan Sashen Ciniki da Canji, ya sanya wa hannu ta jaddada cewa za a bi ƙa’idojin KYC da binciken kwastomomi sosai.

An kuma ƙayyade ciniki da dala $150,000 a mako ga kowane BDC, tare da umarnin mayar da duk wata dala da ba a yi amfani da ita ba cikin sa’o’i 24.

Haka kuma, an haramta cinikin ɓangare na uku, an ƙayyade biyan kuɗi da tsabar kuɗi zuwa kashi 25% kawai, yayin da sauran dole su bi ta hanyoyin biyan kuɗi wato zamani ta hanyar turansifa, domin tabbatar da sahihanci da bin diddigi.

Sababbin Ƙa’idoji Da Tsarin Aiki

Tier-1 BDCs za su yi aiki a faɗin ƙasa, yayin da Tier-2 za su taƙaita ga jiha ɗaya ko Abuja. An kuma hana bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi mallakar lasisin BDC.

Game da farashin canji, BDCs ba za su wuce ƙarin kashi 1% sama da farashin da suka saya ba.

Sabuwar doka ta kuma ƙayyade cewa ba fiye da kashi 25% na kowace mu’amala za a biya da tsabar kuɗi ba.

Wadatar Dala da Daidaituwar Naira

Masana kamar Bismark Rewane sun bayyana cewa rage giɓin farashin canji alama ce ta samun ingantuwar kasuwa. Ya kuma ƙiyasta cewa naira na iya ƙara daraja idan aka duba tsarin PPP.

Shi ma Shugaban Ƙungiyar ‘Yaj Canji na Nijeriya, Aminu Gwadabe na ABCON, ya ce ƙarin wadatar dala ta BDCs za ta taimaka wajen tabbatar da daidaituwar naira na gode tsawon lokaci.

Ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso, CBN ya faɗaɗa hanyoyin samun dala, ciki har da kuɗaɗen ‘yan ƙasar waje (diaspora remittances), da sabbin masu tura kuɗi (IMTOs).

Ta hanyar haɗa BDCs cikin kasuwar hukuma tare da tsauraran ƙa’idoji, CBN na ƙara wadatar dala, wanzar da gaskiya da sama wa naira natsuwa, har ma da tsarin kuɗin ƙasa baki ɗaya.

Tags: BabbanBankinNijeriyaBDCscanjiCBNOlayemiCardoso
Previous Post

Tinubu ya zartar da umurnin shigar kuɗin mai asusun gwamnati kai-tsaye

Next Post

Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas

Related Posts

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa

May 3, 2026
Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda

May 1, 2026
Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna

May 1, 2026
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Juyin Zamani: Yadda CBN ke ƙarfafa wa ɗalibai koyon ilmin sarrafa kuɗi, yayin da tattalin arziki ke sauyawa a zamanance 

April 30, 2026
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

April 29, 2026
Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna

April 27, 2026
Next Post
Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas

Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!