Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin sa za ta yi nasara kan ta’addanci da ‘yan bindiga, yana mai bayyana matsalar tsaro a matsayin abin da ba za a amince da shi ba kuma ba ya cikin ɗabi’un al’ummar ƙasar nan.
Shugaban ya ce rashin tsaro ya zama babban ƙalubale ga zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin ƙasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake buɗe taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) karo na biyu da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa a yau Litinin.
Ya ce gwamnatin sa ta ƙudiri aniyar ƙarfafa jami’an tsaro tare da samar da dabarun zamani domin murƙushe ayyukan ta’addanci da fashi da makami a faɗin ƙasar nan.
Shugaban Ƙasar ya jaddada cewa rashin tsaro yana hana bunƙasar tattalin arziki, inda ya ce dole ne a haɗa kai tsakanin gwamnati, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar.
Ya kuma yaba wa gwamnonin jihohin Borno, Katsina da Kaduna bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.
Dangane da tattalin arziki, Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau, ciki har da daidaita tattalin arziki da dawo da amincewar masu zuba jari.
Ya ƙara da cewa jihohi da ƙananan hukumomi yanzu suna samun kaso mafi yawa daga asusun tarayya, lamarin da ke taimaka masu wajen biyan albashi da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
Shugaban ya ce Shirin Cigaban Ƙasa na Renewed Hope 2026–2030 zai mayar da hankali kan noma, bunƙasa sana’o’i, zuba jari a kiwon dabbobi da kuma cigaban bil’adama.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa sakamakon taron NEC zai taimaka wajen samar da cigaba mai ɗorewa da haɗa kowa a faɗin Nijeriya.





