Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin ƙarfafa harkokin noma da inganta samar da abinci a Najeriya, musamman ta hanyar tallafa wa ƙananan manoma.
Haka kuma, ya amince da shirin sake fasalin jarin Bankin Noma na Nijeriya (Bank of Agriculture) zuwa Naira tiriliyan 1.5 domin faɗaɗa damar manoma samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan noma.
Sanarwar da mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Dele Alake, ya fitar a ranar 22 ga Nuwamba, 2026, ta ce shirin tallafin Naira biliyan 250 na Renewed Hope Smallholder Support and Value Chain Fund ya riga ya taimaka wa ƙananan manoma sama da 500,000 a jihohi 16, ciki har da mata sama da 70,000.
An kuma raba buhunan takin zamani kusan miliyan 2.5 da buhunan iri ingantattu 300,000, yayin da shirin ke da burin kai tallafi ga manoma miliyan biyu.
Sanarwar ta ce gwamnati na aiwatar da shirin Guaranteed Minimum Price mai kuɗi Naira biliyan 200 domin kare manoma daga sayar da amfanin gonar su cikin asara.
A ƙarƙashin shirin, Bankin Noma ya sayi tan 170,000 na masara, shinkafa, dawa da rogo.
Haka kuma, an ƙaddamar da shirin tallafa wa manoman albasa tare da haɗin gwiwar ƙungiyar NOPPMAN, wadda ke wakiltar manoman albasa sama da 11,800, domin samar da iri, taki, kuɗaɗen sayen amfanin gona da wuraren ajiya masu amfani da hasken rana.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa shirin noman rani na 2026 na da burin tallafa wa manoma 400,000, tare da samar da damar noman alkama a hekta 120,000 da sauran amfanin gona a hekta 300,000.
Shirin farfaɗo da noman citta ya tallafa wa manoma 3,200 a Kachia ta Jihar Kaduna, yayin da aka tura taraktoci 1,571 zuwa jihohi 23 domin taimaka wa aikin gona a hekta miliyan 1.2.
Gwamnati na kuma shirin tallafa wa mata 50,000 ta hanyar ƙungiyoyin haɗin gwiwa.
Bugu da ƙari, shirin amfani da wutar lantarki wajen bunƙasa noma na Naira biliyan 385 zai samar da babura masu kafa uku na jigilar kaya 44,000 da injinan ban-ruwa masu amfani da hasken rana 100,000, domin tallafa wa iyalan manoma 500,000.
Sanarwar ta ce waɗannan tsare-tsare na daga cikin ƙoƙarin faɗaɗa samar da abinci, ƙarfafa sarƙar darajar amfanin gona da bunƙasa tattalin arzikin noma a ƙasar nan.







