• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
November 17, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sababbin ƙa’idojin da ke tsara yadda bankunan kasuwanci, kamfanonin fasahar hadahadar kuɗi (Fintech) da sauran masu samar da ayyukan biyan kuɗi za su adana, sarrafa da kuma kula da bayanan hada-hadar kuɗaɗen kwastomomin su.

Ƙa’idojin sun shafi bankuna da kamfanoni irin su Access Bank, Zenith Bank, OPay, PalmPay da sauran masu gudanar da harkokin kuɗi da ke ƙarƙashin kulawar CBN.

Babban bankin ya amince wa cibiyoyin kuɗi su ci gaba da amfani da kamfanonin fasaha na waje, ciki har da masu samar da ayyukan Cloud, masu sarrafa biyan kuɗi da sauran kayayyakin more rayuwar fasaha, muddin suna bin dokokin Nijeriya na adana bayanai a cikin ƙasar.

A cikin sabon daftarin tambayoyi da amsoshi da ya fitar, CBN ya bayyana cewa dole ka ne amfani da kamfanonin fasaha na waje ya kasance bisa tsauraran sharuɗɗa, tare da tabbatar da cewa Nijeriya ce ke da iko kan bayanan hada-hadar kuɗi a duk tsawon lokacin da ake amfani da su.

Hukumar ta ce duk wani tallafin fasaha daga nesa, wanda ya haɗa da gyaran matsalolin na’urori, sa ido kan tsaron yanar gizo da magance matsalolin fasaha, sai da amincewar hukumomi.

Haka kuma, dole ne cibiyoyin kuɗi su tabbatar da cewa ba a amfani da damar shiga bayanai daga ƙasashen waje wajen adana, kwafe ko aika bayanan da doka ta tanada zuwa wajen Nijeriya ba tare da izini ba.

CBN ya kuma buƙaci su samar da ingantattun hanyoyin sa ido, taƙaita damar shiga bayanai da kuma kare su daga hare-haren yanar gizo.

Babban bankin ya fayyace cewa ba lallai ne bankuna da kamfanonin Fintech su mallaki ko tafiyar da dukkan kayayyakin more rayuwar fasahar su da kan su ba.

Ya bayyana cewa za su iya amfani da tsarin Public Cloud, Private Cloud, Hybrid Cloud, Community Cloud ko Multi-Cloud, matuƙar sun cika sharuɗɗan adana bayanai a Nijeriya, tsaron yanar gizo da damar hukumomi wajen tantance bayanai.

Wannan na nufin cibiyoyin kuɗi za su iya ci gaba da amfani da ƙwararrun kamfanonin fasaha, amma hakan ba zai rage musu alhakin bin ƙa’idojin CBN ba.

CBN ya bayyana cewa ƙa’idojin sun shafi bayanai da dama, ciki har da adadin kuɗin da aka tura, ranakun hada-hadar kuɗi, lambobin tantance biyan kuɗi, bayanan asusu, lambobin walat ɗin kuɗi, bayanan waɗanda aka tura wa kuɗi da kuma bayanan kammala hada-hadar.

Haka kuma sun shafi bayanan sa ido kan zamba, bayanan tantance ayyuka, ajiyar bayanai na kariya, tsofaffin bayanan hada-hadar kuɗi da tsarin dawo da bayanai idan wata matsala ta faru.

Saboda haka ba wai kawai manyan rumbunan bayanai za a adana a cikin Nijeriya ba, har da dukkan bayanan kariya da na gaggawa da ke ɗauke da bayanan hada-hadar kuɗi.

Hukumar ta buƙaci cibiyoyin kuɗi da su riƙa adana yarjejeniyoyin su da kamfanonin fasaha, bayanan yadda ake sarrafa bayanai da kuma hujjojin da ke tabbatar da bin ƙa’idojin.

CBN ya tabbatar da cewa wa’adin cika waɗannan ƙa’idoji shi ne ranar 1 ga Janairu 2027, ba tare da wani ƙarin lokaci kai-tsaye ko keɓancewa ga tsofaffin yarjejeniyoyin fasaha ba.

Saboda haka dole ne bankuna da kamfanonin Fintech da ke amfani da kayayyakin fasaha ko tsarin Cloud a ƙasashen waje su daidaita tsarin su da sababbin ƙa’idojin kafin wannan wa’adi.

Manufar wannan mataki ita ce ƙara ƙarfafa sa ido kan harkokin kuɗi, inganta tsaron bayanan kwastomomi da kuma tabbatar da cewa dukkan bayanan hada-hadar kuɗaɗen da suka shafi Nijeriya suna ƙarƙashin ikon hukumomin ƙasar.

Tags: bankunaCBNƙa'idoji
Previous Post

Katsina 2027: Ɗanmarke ya naɗa tsohon kakakin soji Sagir Musa daraktan yaƙin neman zaɓe

Next Post

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya

November 16, 2026
Next Post
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!