• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

EFCC ta gurfanar da mutum biyu a kotu kan zargin damfarar samun aikin NNPC na naira miliyan 600

ALI KANO by ALI KANO
February 9, 2026
in Labarai
A A
0
EFCC ta gurfanar da mutum biyu a kotu kan zargin damfarar samun aikin NNPC na naira miliyan 600
Giɗaɗo Ibrahim, wanda ake zargi

Giɗaɗo Ibrahim, wanda ake zargi

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Tattalin Arziki (EFCC), a yau Litinin ta gurfanar da Giɗaɗo Ibrahim da Halimat Adenike Tejusho (wadda ta gudu ta ɓoye) a gaban Mai Shari’a H. Mu’azu na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT), da ke Maitama, Abuja, kan zargin damfarar samun aiki har naira miliyan 600.

An gurfanar da su kan gyaran tuhume-tuhume guda shida da suka shafi zamba, karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da kuma jabun takardu, har zuwa adadin N603,400,000.00 (Naira miliyan ɗari shida da uku da dubu ɗari huɗu).

A zaman kotun na yau, lauyan masu gabatar da ƙara, Y. Tarfa, ya ja hankalin kotu kan gyaran tuhume-tuhume guda shida, inda ya roƙi kotun da ta ba wanda ake zargi damar amsa laifin.

Tuhuma ta farko ta ce: “Kai, GIƊAƊO IBRAHIM da HALIMAT ADENIKE TEJUSHO O (wadda ta gudu a halin yanzu), tsakanin watan Agusta 2024 zuwa Oktoba 2024 a cikin hurumin wannan kotu mai daraja, kun karɓi kuɗi har N603,400,000.00 (Naira miliyan ɗari shida da uku da dubu ɗari huɗu) daga OLUSEYE YOMI-SHOLOYE, ta hanyar yaudara da cewar za ku taimaka mata ta zama Manajan Darakta Janar (GMD) ta Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), alhali kun san wannan magana ƙarya ce. Ta haka kun aikata laifi da ya saɓa wa Sashe na 1(a) na Dokar Damfarar Kuɗin Gaisuwa (Advance Fee Fraud) da Sauran Laifuffukan da suka Shafi Zamba ta 2006, wanda ake hukunta shi a ƙarƙashin Sashe na 1(3) na dokar.”

Tuhuma ta biyu kuma ta ce: “Kai, GIDADO IBRAHIM, a watan Agusta 2024 a Abuja, a cikin hurumin wannan kotu mai daraja, ka yi amfani da wata takarda ta jabu mai taken ‘Presidential Villa State House, OFFICE OF THE NATIONAL SECURITY ADVISER’ a matsayin sahihiya, alhali ka sani ko kuma ya kamata ka sani cewa takardar jabun ce. Ta haka ka aikata laifi da ya saɓa wa Sashe na 366 na Dokar Final Kod, wanda ake hukunta shi a ƙarƙashin Sashe na 364 na dokar.”

Wanda ake tuhumar dai ya musanta dukkan tuhume-tuhume guda shida lokacin da aka karanta masa su.

Bayan ya musanta laifin, sai lauyan masu gabatar da ƙara, Tarfa, ya roƙi kotu da ta sanya ranar fara shari’a tare da bayar da umurnin tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.

Sai dai lauyan wanda ake tuhuma, B.B. Alhaji, ya sanar da kotu cewa ya shigar da takardar neman beli, yana mai cewa ko da yake ba a kai ga sauraron ta ba tukuna, ya kamata a tsare wanda ake tuhuma a hannun EFCC idan an yi la’akari da yanayin lafiyar sa, har zuwa ranar sauraro da yanke hukunci kan neman belin.

Mai Shari’a Mu’azu ya ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Fabrairu, 2026 domin sauraron buƙatar belin, tare da bayar da umurnin a tsare wanda ake tuhuma a Gidan Gyaran Hali na Kuje.

Tags: EFCCGiɗaɗoIbrahimHalimatAdenikeTejushokotukurkukuMaiShari’aHMu’azuzamba
Previous Post

Tinubu ya sha alwashin kawo ƙarshen ta’addanci da ‘yan bindiga

Next Post

Taron NEC na 2026: Gwamnan CBN ya yi gargaɗin barazanar yawan kuɗi da guguwar zaɓen 2027 kan nasarorin tattalin arziki da aka sha wahalar samu

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Taron NEC na 2026: Gwamnan CBN ya yi gargaɗin barazanar yawan kuɗi da guguwar zaɓen 2027 kan nasarorin tattalin arziki da aka sha wahalar samu

Taron NEC na 2026: Gwamnan CBN ya yi gargaɗin barazanar yawan kuɗi da guguwar zaɓen 2027 kan nasarorin tattalin arziki da aka sha wahalar samu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!