• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya rattaba hannu a dokar kafa cibiyoyin horas da ‘yan sanda

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 9, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya rattaba hannu a dokar kafa cibiyoyin horas da ‘yan sanda
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa Cibiyoyin Horas da ‘Yan Sanda, wadda aka amince da ita a shekarar 2024 domin bai wa cibiyoyin horaswa na ‘yan sanda doka da cikakken tsarin aiki.

Dokar ta bada sahalewar kafa cibiyoyi 48 na horaswa a faɗin ƙasar nan tare da gina tsarin koyarwa, bincike da horaswa da zai tabbatar da ingantaccen aiki da bin ƙa’idodin duniya a harkar tsaro.

An kafa dokar ne bisa ƙudirin Sanata Ahmed Malam-Madori (na jam’iyyar APC mai wakiltar Jigawa Arewa Maso Gabas), wanda ya bayyana cewa manufar ita ce inganta ilimi, ƙwarewa da gogewar aikin ‘yan sanda.

Dokar ta tanadi nau’o’in cibiyoyi guda biyar da suka haɗa da Kwalejojin ‘Yan Sanda, Makarantun Horaswa, Makarantun Dabarun Aiki, Makarantun Fasaha, da Cibiyoyi na Musamman.

Wasu daga cikin fitattun cibiyoyin da dokar ta amince da su sun haɗa da KWalejin ‘Yan Sanda ta Ikeja, Kaduna, Maiduguri, Jos, Oji River, da Kwalejin bincike ta Inugu.

Haka kuma dokar ta amince da cibiyoyin horaswa a Bauchi, Minna, Sokoto, Benin, Kalaba, Ilorin, Ibadan, Jos, da wasu wurare don faɗaɗa horaswa a matakin ƙasa.

A ƙarƙashin dokar, Makarantun Dabarun Aiki za su rika koyar da dabaru na musamman ga rukunin “Mobile Police” da “Counter-Terrorism Unit”, inda aka amince da makarantun a Gwoza, Ila-Orangun, Ende-Hill, Nonwa-Tai, da Gombe. Haka nan akwai makarantun a Kafin Hausa, K9 School a Bukuru, da Mounted Troop School a Jos.

Sanata Malam-Madori ya bayyana amincewar Shugaban Ƙasa da dokar a matsayin mataki mai girma da zai sauya tsarin tsaro a ƙasar nan.

Tags: 'yan sandakwalejojiSanata Ahmed Malam-MadoriShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya mallaki fiye da dala biliyan 1

Next Post

Dalilan da suka haifar da jan-ƙafa wajen aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 – Yakubu

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Dalilan da suka haifar da jan-ƙafa wajen aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 – Yakubu

Dalilan da suka haifar da jan-ƙafa wajen aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 - Yakubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!