Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kira taro na musamman na Majalisar Koli ta Ƙasa (Council of State) da Majalisar ‘Yan Sanda (Police Council) domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a sassan ƙasar nan da sauran manyan batutuwan ƙasa.
Taron, wanda za a gudanar a ɗakin taro na Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a gobe Alhamis, na nuna sabon ƙudirin Tinubu na ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da dawo da ƙwarin gwiwar ‘yan kasa kan ƙoƙarin gwamnati wajen magance matsalar rashin tsaro.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ofishin Harkokin Majalisar, Dakta Emanso Umobong, ya fitar a madadin Sakataren Gwamnatin Tarayya, an bayyana cewa an gayyaci membobin majalisun biyu su halarci zaman ko dai kai-tsaye ko ta yanar gizo.
Sanarwar ta ce, “Taron zai mayar da hankali ne kan muhimman lamurran ƙasa, musamman waɗanda suka shafi tsaro da aikin ‘yan sanda. Za a fara taron Majalisar Ƙoli da ƙarfe 1:00 na rana, sannan taron Majalisar ‘Yan Sanda zai biyo bayan haka da ƙarfe 2:00 na rana.”
Majalisar Ƙoli ta Ƙasa, wadda Shugaban Ƙasa ke jagoranta, ta ƙunshi tsofaffin shugabanni, tsofaffin Alƙalan Alƙalai, gwamnoni da kuma Ministan Shari’a. Ita ce ke bada shawarwari kan manyan manufofin gwamnati, musamman batutuwan tsaro da naɗin muƙamai.
Ita kuwa Majalisar ‘Yan Sanda, tana da alhakin kula da yadda ake gudanar da ayyuka da tsarin shugabanci na Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, ciki har da naɗin manyan jami’ai da ladabtar da su.
Wata majiya a Fadar Shugaban Ƙasa ta shaida wa jaridar PUNCH cewa tarurrukan za su yi nazari kan halin tsaro a ƙasar, su tantance cigaban da ake samu a harkokin soji da tsare-tsare, tare da fitar da sababbin matakai don daƙile ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci da ke addabar wasu jihohin Arewa da tsakiyar ƙasar nan.
Taron zai kuma haɗu da tattaunawa kan wasu muhimman batutuwan siyasa, ciki har da zaɓen wanda zai gaji shugaban hukumar INEC mai barin gado.
Taron Majalisar Ƙoli na wannan makon zai kasance na biyu tun bayan hawan Tinubu mulki, kuma ana sa ran zai sanya sabon salo wajen haɗa kai tsakanin jihohi da tarayya don magance matsalolin tsaro da ke damun ƙasar nan.







