• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta zuba jarin dala miliyan 220 don samar da ayyukan yi — Shettima

Wakilin Mu by Wakilin Mu
October 22, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya za ta zuba jarin dala miliyan 220 don samar da ayyukan yi — Shettima
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a wajen ƙaddamar da shirin Nigeria Jubilee Fellows Programme (NJFP) 2.0 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a yau.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a wajen ƙaddamar da shirin Nigeria Jubilee Fellows Programme (NJFP) 2.0 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a yau.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a wajen ƙaddamar da shirin Nigeria Jubilee Fellows Programme (NJFP) 2.0 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a yau

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin zuba jarin dalar Amurka miliyan 220 domin samar da sababbin damarmakin ayyukan yi ga matasan ƙasar nan.

 

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana haka a yau Laraba yayin ƙaddamar da shirin Nigeria Jubilee Fellows Programme (NJFP) 2.0 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

 

Shirin, wanda aka haɗa gwiwa da Tarayyar Turai (EU) da Asusun Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), na nufin haɗa matasa masu ƙwarewa da dama ta fannin horo, gogewa da kuma jagoranci (mentorship), domin taimaka musu su shiga sahun masu dogaro da kai.

 

Shettima ya ce burin gwamnati shi ne rage tazara tsakanin karatu da samun aiki, ta hanyar bai wa matasa damar amfani da ilimin da suka samu wajen gina tattalin arziƙin ƙasa.

 

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da cewa shirin ya samu tallafi kai tsaye daga kasafin kuɗi na ƙasa, tare da buɗe “NJFP Basket Fund” domin samar da hanyoyin samun kuɗaɗen da za su dore.

 

Mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga masu zuna jari masu zaman kansu, ƙungiyoyin ci gaba da masu ba da gudummawa su haɗa kai wajen tabbatar da nasarar shirin.

 

Ya bayyana cewa gwamnati za ta tabbatar da adalci da haɗin kai wajen aiwatar da mataki na biyu na shirin, domin ya shafi matasa daga kowane yanki da bangare na ƙasa, musamman a fannoni kamar noma, makamashi, fasahar zamani, masana’antu da kuma harkokin kirkire-kirkire.

 

Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana NJFP 2.0 a matsayin ci gaba daga nasarorin da aka samu tun 2021, inda sama da matasa 13,000 suka amfana da horo da ayyuka.

 

Ya ce gwamnati na da burin samar wa matasa 100,000 aiki cikin shekaru biyar masu zuwa.

 

Jakadiyar UNDP a Najeriya, Ms Elsie Attafuah, ta ce haɗin gwiwar da ake da EU da UNDP ta samar da damammaki da ta kai sama da matasa 40,000 cikin fannoni daban-daban na tattalin arziƙi.

Ita ma jakadiyar Tarayyar Turai a Najeriya, Gauthier Mignot, ta ce EU na fatan ganin NJFP 2.0 ya zama ɓangare na tsarin gwamnati, domin tabbatar da dorewarsa.

Previous Post

Tinubu ya amince a ba ƙananan ’yan kasuwa tallafin N250,000 a Katsina

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Jihar Neja Bisa Fashewar Tankar Mai a Essa

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Jihar Neja Bisa Fashewar Tankar Mai a Essa

Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Jihar Neja Bisa Fashewar Tankar Mai a Essa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!