• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 3, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa
Daga dama: Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da Shugabar Hukumar Sa-ido da Bibiyar Safarar Kuɗaɗe (NFIU), Hafsat Abubakar Bakari, lokacin da ta kai wa gwamnan ziyarar aiki a hedikwatar CBN, a ranar 23 ga Afrilu, 2026, a Abuja

Daga dama: Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da Shugabar Hukumar Sa-ido da Bibiyar Safarar Kuɗaɗe (NFIU), Hafsat Abubakar Bakari, lokacin da ta kai wa gwamnan ziyarar aiki a hedikwatar CBN, a ranar 23 ga Afrilu, 2026, a Abuja

Cikin makon jiya ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da wani faifan bidiyo mai ɗauke da bayanan sigogi da illolin laifukan karkatar da kuɗaɗe ga ƙasar nan da kuma tattalin arzikin ta.

Bidiyon mai ɗauke da bayanan mintina kusan shida, ya kuma ƙunshi irin hukuncin da doka ta tanadar wa masu aikata laifukan karkatar da kuɗaɗe. Haka kuma ya zayyana dalla-dalla irin ƙoƙarin da CBN haɗi da hukumomin EFCC da NFIU ke yi wajen sa-ido, bibiya, bankaɗowa da zaƙulo wuraren da ake karkatar da kuɗaɗen.

CBN ya bayyana aikin musamman da Sashen Bankaɗo Kuɗaɗen da aka Karkatar ta Hanyar Harƙalla (SCUML) ke yi, wato ‘Special Control Unit against Money laundering’.

Wannan sashe dai ya maida hankali ne wajen bibiya da sa-ido kan wasu manyan wuraren da ake hahahadar manyan kuɗaɗe, waɗanda ba cibiyoyin hadahadar kuɗi ba ne. Wato kamar manyan dillalan manyan gidaje da kadarori, manyan lauyoyi, manyan masu sayar da kayan alatu na alfarma masu tsada, kantinan hadahada na zamani, ‘wato super market’, manyan gidajen raƙashewa da gidajen caca da sauran su.

Sanarwar CBN ta ce dukkan irin waɗannan wurare da ma wasu da za a lissafa a ƙasa, duk wurare ne da ake karkatar da kuɗaɗen da aka mallaka ta haramtacciyar hanya.

Sigogi, Illoli da Hukunce-hukunce Kan Harƙallar Karkatar da Kuɗaɗe:

Harƙallar karkatar da kuɗaɗe da aka sani da ‘money laundering’, hanya ce da ake karkatar da kuɗaɗen da aka samu ko aka tara ta haramtacciyar hanya, inda ake shigar da su cikin wata harka ko hadahada ta yadda a ido za a riƙa yi masu kallon kuɗaɗen da aka tara ta halattacciyar hanya.

Irin kuɗaɗen da ake karkatarwar sun ƙunshi kuɗaɗen da aka tara ta hanyar safarar muggan ƙwayoyi, kuɗaɗen zamba, kuɗaɗen damfara, kuɗaɗen rashawa da cin hanci, kuɗaɗen da aka karkatar don kauce wa biyan haraji da sauran su.

Hanyar farko da ake bi wajen karkatar da irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe ita ce ta hanyar kimshe a bankuna ko ta hanyar sayen manyan kadarori da kuɗin.

Akwai kuma hanya ta biyu, wato ta hanyoyin riƙa tuttura kuɗaɗen a hadahadar kamfanonin ɗanyen mai irin su Shell, kimshe su a asusun ajiyar kuɗaɗen hadahadar ɗanyen mai a ƙasashen waje ta hanyar ɓoye salsalar harƙallar da aka yi har aka tara kuɗaɗen. Ana yin haka ne da nufin wai don kada hukuma ta zaƙulo inda aka kimshe kuɗaɗen.

Hanya ta uku kuwa ita ce hanyar sake narka kuɗaɗen cikin ƙasa, ta yadda za a riƙa yi masu kallon halastattun kuɗaɗe. Wato zai a zuba su matsayin hannun jari, ko a riƙa gina maka-makan rukunin gidaje ko manyan cibiyoyin kasuwanci wato ‘plaza’ da sauran hanyoyin kasuwanci.

Kaɗan daga illolin harƙallar karkatar da kuɗaɗe ita dakushe kaifi da ƙarfin cibiyoyin hadahadar kuɗi, kambama cin hanci da rashawa, yawaita masu aikata laifukan zamba, sai kuma kawo naƙasu ga tsarin hadahadar kuɗi ga ƙasa ɗungurugum.

Harƙallar karkatar da kuɗaɗe na kawo illa sosai ƙasa, ta hanyar cusa shakku ga masu zuba jari cikin ƙasa daga ƙasashen waje, kuma yana yi wa tattalin arziki mummunan zagon-ƙasa.

Dalili kenan hukumomi irin su EFCC, NFIU da kuma uwa-uba CBN ba su ɗauki shirin daƙile harƙallar karkatar kuɗaɗe da wasa ba. Ita kan ta dokar Nijeriya ta tanadi hukumcin ƙwace dukiya, ɗauri na dogon zango da tara mai tsanani ga duk wanda aka kama da laifin harƙallar karkatar da kuɗaɗe.

Tags: CBNOlayemi Cardoso
Previous Post

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

Next Post

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!