• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu na so gwamnoni su tallafa wa talakawa, su ƙarfafa marasa galihu

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 23, 2026
in Siyasa
A A
0
Tinubu na so gwamnoni su tallafa wa talakawa, su ƙarfafa marasa galihu
Shugaba Tinubu tare da gwamnonin a wajen buɗa-bakin

Shugaba Tinubu tare da gwamnonin a wajen buɗa-bakin

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci da su ƙara karkata manufofin su wajen tallafa wa talakawa da marasa galihu, domin a cewar sa cigaba ba zai yi ma’ana ba idan bai kai har matakin ƙasa ba.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da ya karɓi baƙuncin gwamnonin jihohi domin buɗa-baki na haɗin gwiwar addinai.

Ya ce haɗuwar azumin Ramadan da na Kiristoci (Lent) a lokaci guda alama ce ta ɗan’adamtaka ɗaya, wadda ke buƙatar juriya, sadaukarwa da ƙaunar juna.

Shugaban ya bayyana cewa watan Ramadan da lokacin Lent dama ce ga shugabanni su sake duba halin da jama’a suke ciki, musamman matasa da marasa galihu, tare da ƙirƙiro shirye-shiryen da za su shafi rayuwar su kai-tsaye.

Ya jaddada cewa duk da nasarorin da aka samu, akwai sauran aiki mai yawa a fannin rage talauci da ƙarfafa wa matasa.

A jawabin sa, shugaban ya buƙaci gwamnonin su kasance masu haƙuri da juna, su gina tsari a wannan lokaci na ban-gaskiya da haɗin kai, tare da bai wa matasa damar numfasawa.

Ya kuma yi maraba da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya yi masa maraba cikin raha.

Haka nan, Tinubu ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, bisa nuna karamci ga Musulmi da Kiristoci a lokacin azumi, musamman ta hanyar shirye-shiryen tallafin Ramadan da suka shafi kowa ba tare da la’akari da addini ba.

Shugaban ya sake nanata aniyar sa ta ƙarfafa tsaro a ƙasar nan, inda ya ce gwamnati ba za ta jinkirta cika alƙawarin kafa ‘yan sandan jihohi ba domin a magance matsalar rashin tsaro.

Ya ce tsaro shi ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki, domin noma, kasuwanci da zaman lafiya su bunƙasa.

Tinubu da gwamnoni a taron shan ruwan

Da yake jawabi a madadin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya yaba wa Shugaba Ƙasa bisa yadda yake ƙarfafa haɗin kan ‘yan ƙasa duk da bambance-bambancen addini da ƙabila.

Ya ce haɗuwar azumin Ramadan da Lent abu ne na musamman da Allah ya tsara domin tunatar da Musulmi da Kiristoci muhimmancin haɗin kai da tausayi.

Uzodimma ya ƙara da cewa shugabancin Tinubu ya kawo sauye-sauye masu muhimmanci a siyasar ƙasar nan, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnonin jihohi.

Ya ce wannan lokaci na azumi lokaci ne na taimakon marasa galihu, kuma taron buɗa-baki na haɗin kan addinai alama ce ta wannan ruhi na haɗin kai.

Tags: addinaibuɗa-bakigwamnoniLentRamadanTinubu
Previous Post

El-Rufai ya yi ƙarar ICPC kan binciken da ta yi a gidan sa

Next Post

Ba mu biya kuɗin fansa don a sako ɗaliban Neja ba – Gwamnatin Tarayya

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai

Ba mu biya kuɗin fansa don a sako ɗaliban Neja ba - Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!