• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Nagartattun sauye-sauyen CBN kan manufofin tattalin arziki sun haddasa ambaliyar masu sha’awar zuba jari daga ƙasashen waje

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 14, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Sauye-sauyen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Olayemi Cardoso, sun taimaka matuƙa wajen dawo da sha’awar masu zuba jari na ƙasashen waje a ɓangaren saka kuɗaɗe a kadarorin Nijeriya, ta hanyar dawo da ƙwarin gwiwa ga tsarin hadahadar kuɗi na a cikin ƙasa.

Haka kuma yin amanna dangane da yadda ake tsara shirye-shiryen manufofin kuɗi bisa gaskiya, da kuma tabbatar da daidaito a kasuwar musayar kuɗaɗen waje, su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen antayo wasu zuba jari cikin Nijeriya daga waje.

Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen shi ne sassautawa da kuma haɗe tsarin musayar kuɗaɗen waje zuwa kasuwar musayar kuɗi ta bai-ɗaya. Kafin waɗannan gyare-gyare, yawaitar farashin musayar kuɗaɗe daban-daban da kuma ƙarancin dala sun hana masu zuba jari daga ƙasashen waje shiga kasuwannin zuba jari a Nijeriya, saboda tsoron rashin samun damar mayar da ribar su zuwa ƙasashen su.

Matakin da CBN ya ɗauka na komawa tsarin da kasuwa ke ƙayyade farashin musayar kuɗaɗe, tare da ƙoƙarin kawar da giɓin buƙatar kuɗaɗen waje, ya rage rashin tabbas tare da inganta yawan kuɗaɗen da ke zagayawa a matsayin kuɗaɗen hadahada a kasuwar musayar kuɗaɗe.

Waɗannan sauye-sauye sun kuma ƙarfafa amincin tattalin arzikin Nijeriya.

Sai kuma tsauraran manufofin hadahadar kuɗi da ƙarin kuɗin ruwa sun sanya takardun baitulmalin gwamnati da takardun bashi na Nijeriya suka zama masu jan hankali ga masu zuba jari daga ƙasashen waje da ke neman riba mai yawa a kasuwannin ƙasashe masu tasowa.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa masu zuba jari sun ƙara nuna sha’awar dawowa Nijeriya saboda kasuwar kuɗaɗen waje ta fi samun tsari da kuma tabbaci a yanzu.

Yayin da ƙwarin gwiwa ya karu, kuɗaɗen da ke shigowa cikin Nijeriya daga waje sun ƙaru sosai.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa kuɗaɗen da suka shigo Nijeriya sun ƙari da kusan kashi 90 cikin 100 a shekarar 2025, inda suka kai dala biliyan 23.22, wanda akasari ya fito daga masu zuba jari na ƙasashen waje da suka saka kuɗaɗe a takardun bashi.

Kayan kasuwar kuɗi da kuma hannayen jari

Ɓangaren bankuna ya kasance ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka amfana da dawowar ƙwarin gwiwar masu zuba jari. Rahotanni sun nuna cewa bankunan Nijeriya sun tara kusan naira tiriliyan 4.61 a ƙarƙashin shirin ƙarfafa jariin bankuna, inda kusan kashi 27 cikin 100 ya fito daga masu zuba jari na ƙasashen waje.

Sannan kuma shiga kasuwar hadahadar hannayen jarin Nojeriya daga ƙasashen waje ta farfaɗo sosai.

Bayanai daga ‘Nigerian Exchange Group’ sun nuna cewa masu zuba jari daga ƙasashen waje sun sayi hannayen jarin Nijeriya da suka haura naira tiriliyan 1 cikin watanni tara na farkon shekarar 2025, wanda ya nuna babban ƙarin shiga idan aka kwatanta da shekarun baya.

Wani babban abu da ya ƙara ƙwarin gwiwar masu zuba jari shi ne ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen ƙetare na Nijeriya.

CBN ya bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta kai kusan dala biliyan 45.5 zuwa kartshen shekarar 2025, abin da ya taimaka wajen daidaita darajar naira tare da tabbatar wa masu zuba jari cewa ƙasar na da ikon cika alƙawurran ta na ƙasashen waje.

Masana harkokin kuɗi da hukumomin tantance matsayin tattalin arziki sun kuma yi maraba da waɗannan gyare-gyare. Kamar kuma yadda rahotanni suka nuna cewa haɗarin kasadar zuba jari a Nijeriya ya ragu yayin da sauye-sauyen suka dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari.

Za a iya fahimtar cewa sauye-sauyen CBN sun taimaka wajen sauya yadda masu zuba jari ke kallon Nijeriya daga kasuwar da ake ganin tana da haɗari da kasadar rashin tabbas a manufofi zuwa ƙasa mai ƙoƙarin dawo da amincewa ta hanyar gyare-gyaren da suka dace da tsarin kasuwa, ingantaccen tsarin kulawa, ƙarin tsare-tsare na gaskiya a harkar kuɗaɗen waje, da kuma tsauraran manufofin hadahadar kuɗi.

Duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale kamar hauhawar farashi, biyan basussuka da matsalolin rashin ingantattun ababen more rayuwa, masu zuba jari da dama yanzu suna ganin kadarorin Nijeriya sun fi jan hankali da sauƙin shiga fiye da yadda suke a baya.

Tags: CBNOlayemi Cardososauye-sauyezuba jari
Previous Post

Kotu a Amurka ta ɗaure farfesa ‘yar Nijeriya watanni 70 kan satar dala miliyan 1.4

Next Post

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

Abin Da Sauyin Talbijin Zuwa Tsarin Dijital A Nijeriya Yake Nufi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!