• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Sufeto-Janar ya naɗa Orvenonne Ikwen kodinetar yaƙi da ƙungiyoyin asiri da ‘yan daba ta ƙasa 

Fatima Abdullahi by Fatima Abdullahi
November 23, 2025
in Labarai
A A
0
Sufeto-Janar ya naɗa Orvenonne Ikwen kodinetar yaƙi da ƙungiyoyin asiri da ‘yan daba ta ƙasa 
SP Orvenonne Ikwen shugabar yaƙi da ƙungiyoyin asiri da 'yan daba ta ƙasa 

SP Orvenonne Ikwen shugabar yaƙi da ƙungiyoyin asiri da 'yan daba ta ƙasa 

Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya naɗa SP Orvenonne Ikwen a matsayin sabuwar Kodinetar Yaƙi da ’Yan Daba da Sauran Ayyukan Ɓatagari ta Ƙasa (POCACOV).

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda a Hedikwatar ’Yan Sanda, Abuja, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana naɗin da cewa wani muhimmin shiri ne na rundunar ’yan sanda ta Nijeriya da aka ƙirƙira domin inganta hanyoyin sulhu da ba na tashin hankali ba wajen yaƙar matsalar ƙungiyoyin ’yan daba da sauran miyagun ɗabi’u a cikin al’umma.

Ya ce: “Wannan naɗi ya yi daidai da ƙudirin IGP na samar da aikin ’yan sanda na zamani, wanda ke dogara da bayanan sirri, fasaha, da kuma mayar da jama’a a tsakiyar aikin tsaron ƙasa, tare da fifita rigakafin laifi, amincewar jama’a, da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’umma.”

Ita dai SP Ikwen, wadda ƙwararriyar jami’ar ’yan sanda ce, gogaggiya a harkokin tsaro da cigaban al’umma, ƙwararriya ce a fannin dabarun sadarwa.

Hundeyin ya ce ta zo da ƙwarewa mai zurfi ta aiki da ilimi a wannan sabon matsayi.

Tana da digirin digirgir (Ph.D.) a fannin Kimiyyar Kwamfuta, ta musamman a Artificial Intelligence da Data Science daga Jami’ar Kalaba.

Ta yi fice wajen gudunmawar da ta bayar a fannin aikin ’yan sanda mai dogaro da fasaha, hulɗa da jama’a, da sadarwar canjin halayya.

Memba ce a Institute of Strategic Management of Nigeria (ISMN) da Institute of Conflict Management & Negotiation Analyst (ICMNA).

Ta taka muhimmiyar rawa a ayyukan sauya fasalin rundunar ’yan sanda, bincike, da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin hukumomi.

Ya ƙara da cewa, “A matsayin ta na Kodineta ta Ƙasa, ana sa ran SP Ikwen za ta faɗaɗa kuma zurfafa ayyukan POCACOV a cikin jami’o’i, makarantun sakandare, al’ummomi, da ƙungiyoyin matasa wajen magance matsalolin ’yan daba, shaye-shaye, barazanar yanar gizo, cin zarafin jinsi, yaɗa bayanan ƙarya, da sauran munanan ɗabi’u ta hanyoyi na rigakafi, haɗin kai, da dabarun da ke mayar da al’umma a gaba.

“Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya yi kira ga SP Ikwen da ta yi amfani da sababbin dabaru na rigakafin laifi, tare da haɗa kai da ɓangarori daban-daban — shugabannin al’umma, makarantu, ƙungiyoyin matasa, da abokan haɗin gwiwa da suka daɗe suna goyon bayan wannan shiri.”

Tags: 'yan daba'yan sandaIGPSP Orvenonne Ikwenƙungiyoyin asiri
Previous Post

Dakarun ‘Operation Zafin Wuta’ sun damƙe ƙasurgumin ɗan bindiga a Wukari

Next Post

Tinubu ya janye ‘yan sanda daga gadin manyan mutane zuwa aikin samar da tsaro

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Tinubu ya janye ‘yan sanda daga gadin manyan mutane zuwa aikin samar da tsaro

Tinubu ya janye 'yan sanda daga gadin manyan mutane zuwa aikin samar da tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!