• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Rarara ya ci amanar mu a zamanin Buhari, da in bi shi gara in mutu – Iyan-Tama

MUKHTAR YAKUBU by MUKHTAR YAKUBU
June 24, 2026
in Labarai
A A
0
Rarara ya ci amanar mu a zamanin Buhari, da in bi shi gara in mutu – Iyan-Tama
Iyan-Tama da Rarara

Iyan-Tama da Rarara

FITACCEN dattijo a Kannywood, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya bayyana matsayin sa kan ce-ce-ku-cen siyasar da suka dabaibaye masana’antar, musamman kalaman da wasu ‘yan fim suke yi cewa dukkan masu harkar fim suna goyon bayan tafiyar mawaƙin siyasa Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) da kuma jam’iyyar APC.

Iyan-Tama ya ce ba gaskiya ba ne a ce dukkan ‘yan fim suna tare da APC, yana mai jaddada cewa kowane mutum yana da nasa ra’ayin siyasa.

Ya yi wannan kalamin ne a wata hira da aka yi da shi a shafin onlayin na ‘Ɗan’uwa Rano TV’ a Kano.

Ya ce: “Ni uba ne a cikin harkar fim, shi kuma Rarara yaron mu ne. Saboda haka, ba dukkan mu ne ‘yan APC ba. Kowa yana da ra’ayin sa. Ni dai ba zan yi tafiyar Rarara ba. Da na yi tafiyar Rarara gara na mutu.”

Ya ci gaba da cewa, “Rarara ɗin nan ni ne na kai shi tafiyar Muhammadu Buhari, amma daga baya ya ci amanar mu, domin ya cuce mu. Akwai mutanen da zan iya zaɓa a cikin APC, amma ni ba na cikin jam’iyyar.”

Dangane da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuwa, Iyan-Tama ya ce ba ya cikin masu goyon bayan sake zaɓen sa.

Ya ce: “Ni ba zan zaɓi Tinubu ba, domin tambayoyin da muka yi tun lokacin zaɓen sa har yanzu ba mu samu amsoshin su ba. Kowa yana ganin yadda matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a Arewa, amma an kasa magance ta. Abin da ba a iya yi wa magani tsawon shekaru ba, sai yanzu da ake tunkarar zaɓe ake cewa za a shawo kan sa. Don haka ni ba na tafiyar Tinubu, kuma ba zan zaɓe shi ba.”

Da aka tambaye shi game da yiwuwar goyon bayan sa ga Peter Obi ko Rabi’u Musa Kwankwaso, jarumin kuma furodusa ya ce shi masoyin Kwankwaso ne, amma ba zai mara wa Obi baya ba.

Ya ce: “Ni masoyin Kwankwaso ne saboda na yarda cewa mutum ne nagari. Amma ba zan yi tafiyar Obi ba, kuma duk wanda nake da tasiri a kan sa ba zan ƙarfafa masa ya zaɓi Obi ba. Sai dai hakan ba yana nufin ba zai iya cin zaɓe ba idan Allah ya ƙaddara masa.”

Tags: Dauda Abdullahi Kahutu RararaHamisu Iyan-TamaKannywoodsiyasaZaɓen2027
Previous Post

An ƙaddamar da aikin samar da ruwan sha a Karu da kewaye a Abuja

Next Post

Cardoso ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Cardoso ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN

Cardoso ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!