Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a yau Litinin ya ƙaddamar da aikin samar da ruwan sha na garin Karu da wasu yankunan da ke kewaye da shi, wanda zai samar da tsaftataccen ruwan sha ga dubban mazauna yankin.
A wata sanarwa da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya fitar, ya bayyana cewa aikin ya ƙunshi shimfiɗa bututun ruwan sha na mataki na biyu da na uku mai tsawon fiye da kilomita 194, domin isar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummomin Karu, Orozo, Jikwoyi, Kurudu da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da su.
Ministan ya ce an aiwatar da aikin ne bisa umurnin Shugaba Tinubu na tabbatar da cewa muhimman ayyukan raya ƙasa ba su tsaya a tsakiyar Abuja kaɗai ba, sai sun kai ga al’ummomin da ke bayan gari da suka daɗe suna fama da ƙarancin ababen more rayuwa.
“A watan Agusta na shekarar 2025 ne aka bayar da kwangilar aikin, kuma an kammala shi cikin shekara guda,” inji Wike.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta himmatu wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi jin daɗin jama’a, musamman a ƙauyuka da garuruwan da ke cikin Babban Birnin Tarayya waɗanda suka daɗe suna fama da gibin ababen more rayuwa.
Wike ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa ayyukan raya al’umma a faɗin FCT, musamman a yankunan tauraron birane da suka kasance a baya wajen samun muhimman ayyukan cigaba.
Ya ce kammala aikin samar da ruwan sha a Karu da yankunan da ke kewaye da shi wani babban cigaba ne da zai inganta rayuwar mazauna yankin tare da rage matsalolin rashin tsaftataccen ruwan sha da suka daɗe suna fuskanta.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, shi ne ya wakilci Shugaba Tinubu wajen ƙaddamar da aikin a yau Litinin.







