• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Cardoso ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN

* Ya gargaɗi ’yan Nijeriya su daina wulaƙanta takardun naira

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 24, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cardoso ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN
Olayemi Cardoso

Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ƙaddamar da Ƙungiyar Jakadun Naira na CBN, wani shiri da aka samar domin wayar da kan al’umma, musamman matasa kan muhimmancin kare daraja da martabar takardun Naira da kuma kula da yadda ake amfani da ita.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ƙungiyar da ta ƙunshi ɗaliban makarantun sakandare a Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) Cardoso ya ce, “Darajar Naira ta fi ƙarfin darajar takardar da aka yi ta da shi. Ita ce kuɗin da doka ta amince da su a Nijeriya. Naira na sauƙaƙa harkokin kasuwanci, tallafa wa ayyukan tattalin arziki, ba da damar ajiya da zuba jari, sannan tana nuna asalin ƙasa da ikonmu a matsayinf al’umma.”

Ya ƙara da cewa kowace takardar kuɗi tana ɗauke da tarihin ƙasa, domin tana ƙunshe da hotunan fitattun ’yan Nijeriya, alamomin ƙasa da kuma abubuwan kariya da aka tsara domin tabbatar da amincewar jama’a ga tsarin kuɗin ƙasar nan.

Cardoso ya ci gaba da cewa, “kowane ɗan Nijeriya yana da alhakin girmama Naira.”

Gwamnan na CBN ya bayyana cewa CBN na ci gaba da kashe kuɗaɗe masu yawa wajen samar da tsabtatattun takardun kuɗi masu ƙarfi da kariya domin biyan buƙatun tattalin arzikin ƙasa.

Daga nan sai ya yi gargaɗin cewa lalata takardun kuɗi, yin rubutu a kan su ko rashin kula da su na sa su lalace da wuri, lamarin da ke ƙara tsadar biyan kuɗin sauya su tare da kawo cikas ga ingancin zagayawar kuɗi a ƙasa.

Ya jaddada cewa kare kuɗin ƙasa ba aikin CBN kaɗai ba ne, illa dai “wani nauyi ne na ƙasa da ya rataya a wuyan kowane ɗan Nijeriya.”

Mataimakiyar Gwamnan CBN mai kula da Ayyuka, Emem Usoro, ta bayyana shirin a matsayin wani mataki da ke nuna ci gaba da ƙoƙarin da CBN ɗin ke yi wajen kare ɗaya daga cikin manyan kadarorin ƙasa, wato Naira.

Ta ce, “Duk ƙasa tana alfahari da kuɗin ta, domin ba wai hanyar musayar kaya kawai ba ce, naira na wakiltar ikon ƙasa, kwanciyar hankali na tattalin arziki, amincewar jama’a da kuma haɗin kan al’umma.”

Da take magana kan yadda ake cin zarafin kuɗi, ta ce rubutu a kan takardun Naira, ɗaure su da ƙarfe, watsa su yayin bukukuwa, duƙunƙune su a cikin aljihu da sauran hanyoyin lalata kuɗi suna rage tsawon lokacin da ake mu’amala da su tsakanin jama’a, tare da ƙara tsadar sauya adadin takardun nairar da suka lalace.

Ta bayyana cewa samun sauyi mai ɗorewa zai zo ne ta hanyar ilimantarwa, wayar da kai da kuma gina kyawawan ɗabi’u tun daga ƙuruciya.

Daraktan Ayyukan Kuɗi da Gudanar da Rassa na CBN, Adetona Adedeji, ya ce kare Naira “haƙƙin kowane ɗan Nijeriya ne,” yana mai cewa za a faɗaɗa wannan yaƙin neman wayar da kai zuwa sassa daban-daban na ƙasar domin daƙile munanan ɗabi’un watsa kuɗi a wurin bukukuwa da sauran hanyoyin cin zarafin naira.

Previous Post

Rarara ya ci amanar mu a zamanin Buhari, da in bi shi gara in mutu – Iyan-Tama

Next Post

‘Yan sandan Kaduna sun gurfanar da mutum 24 a kotu kan kisan gillar da aka yi wa wata mata a Maraban Jos

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
‘Yan sandan Kaduna sun gurfanar da mutum 24 a kotu kan kisan gillar da aka yi wa wata mata a Maraban Jos

'Yan sandan Kaduna sun gurfanar da mutum 24 a kotu kan kisan gillar da aka yi wa wata mata a Maraban Jos

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!