• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Bankin Duniya ya yaba da cigaban gyare-gyaren tattalin arziki da Nijeriya ke yi

Fatima Abdullahi by Fatima Abdullahi
February 5, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Bankin Duniya ya yaba da cigaban gyare-gyaren tattalin arziki da Nijeriya ke yi
Ministan Kuɗi da Daidaita Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, tare da Manajan Daraktar Ayyuka na Rukunin Bankin Duniya, Misis Anna Bjerde, da manyan jami'ai a ƙarshen taron

Ministan Kuɗi da Daidaita Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, tare da Manajan Daraktar Ayyuka na Rukunin Bankin Duniya, Misis Anna Bjerde, da manyan jami'ai a ƙarshen taron

Rukunin Bankin Duniya ya yi maraba da cigaban gyare-gyaren da Nijeriya take yi tare da yaba wa Gwamnatin Tarayya kan fayyace manufar ta, yana mai cewa ana samun ƙaruwar amincewa daga kasuwannin duniya da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

Hakan ya bayyana ne daga wani taro da aka gudanar a wannan makon a Abuja tsakanin Ministan Kuɗi da Daidaita Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, da Manajan Daraktar Ayyuka ta Rukunin Bankin Duniya, Misis Anna Bjerde, tare da manyan jami’ai.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan faɗaɗa samar da ingantacciyar wutar lantarki, ƙarfafa harkar noma, hanzarta bunƙasa kayayyakin more rayuwa na dijital, inganta zirga-zirgar kasuwanci, da kuma buɗe ƙofofin zuba jari daga ɓangaren ‘yan kasuwa — waɗanda dukkan su muhimmai ne wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi da gasa.

Misis Bjerde ta sake jaddada goyon bayan Bankin Duniya ga ajandar bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar zuba jari, tare da mai da hankali kan aiwatar da ayyukan more rayuwa da kuma sa hannun ɓangaren ‘yan kasuwa.

Mista Wale Edun yana miƙa kyautar hoto a madubi ga Misis Anna Bjerde, a ƙarshen taron

A jawabin sa, Mista Edun ya bayyana cewa ana samun gagarumin cigaba a muhimman fannoni, sakamakon tsare-tsaren manufofi masu ƙarfi da kuma sabunta mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziki, jawo jari, da samar da ayyukan yi.

Ya kuma sake tabbatar da jagorancin Nijeriya a gyaran fannin makamashi da burin ta na zama cibiyar tattalin arziki ta yankin, tare da goyon bayan rawar da Nijeriya take takawa a matsayin ta na hedikwatar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).

Ɓangarorin biyu sun amince kan hanzarta aiwatar da shirye-shirye, jawo manyan jarin kuɗi, da samar da dama ga yawan al’ummar Nijeriya da ke ƙaruwa.

Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, Malam Mohammed Manga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa taron ya sake tabbatar da sahihiyar alƙiblar tattalin arziki ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ƙaruwar amincewar duniya da shirin gyare-gyaren ƙasar nan yake samu.

“Wannan muhimmin mataki yana nuna jajircewar Nijeriya wajen samun bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa tare da sanya ƙasar a sahun gaba a kasuwannin yankuna da na duniya,” inji shi.

Tags: AnnaBjerdetaroTattalinArzikiWaleEdun
Previous Post

Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya

Next Post

Sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu suna daidaita Nijeriya — Idris

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu suna daidaita Nijeriya — Idris

Sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu suna daidaita Nijeriya — Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!