Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ya samu damar sauraron wata tattaunawar waya da aka yi kutse aka cafke wadda ta shafi mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaron Ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu.
A wata hira da ya yi a shirin “Prime Time” na gidan talbijin na Arise, El-Rufai ya ce “wani ya sa ido” kan wayar Ribaɗu, lamarin da ya ba shi damar jin NSA ɗin yana zargin bayar da umurni ga jami’an tsaro su kama shi.
Ya amince cewa wannan abu da aka yi ya karya doka, ya ƙara da cewa amma gwamnati ma tana yin hakan a kai a kai.
Ya ce: “Ya yi kiran ne saboda mu ma mun saurari kirayen su. Gwamnati tana tunanin su kaɗai ne suke sauraron kiraye-kirayen waya, amma mu ma muna da hanyoyin mu. Ya yi kiran ya bayar da umurnin.
“Wani ya sa ido kan wayar sa. Gwamnati tana sauraron kirayen mu a ko da yaushe ba tare da umurnin kotu ba. Wani ya sa ido kan wayar sa ya sanar da mu cewa ya bayar da umurnin.”
Wannan furuci ya jawo martani daga Temitope Ajayi, babban mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, wanda ya ce a shafin sa na X: “El-Rufai ya amsa a talbijin na ƙasa cewa wani ya sa ido kan wayar NSA domin ya saurari tattaunawar sa.
“Lokacin da Charles Aniagolu, mai gabatar da hirar, ya katse masa hanzari da cewa wannan aiki ne ba bisa ƙa’ida ba fa, sai El-Rufai ya amince da hakan.
“Yanzu da za a kama shi a ce ya fito da mutumin da ya sa ido kan wayar NSA ba bisa ƙa’ida ba ɗin, cewa zai yi Shugaba Tinubu ‘azzalumi’ ne kuma yana musguna masa.”







