Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana ajiye muƙamin sa ba tare da ɓata lokaci ba.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce Badaru ya sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata na yau 1 ga Disamba cewa ya yanke shawarar janyewa daga kujerar minista ne domin mayar da hankali kan lafiyar sa.
Shugaban Ƙasa ya amince da murabus ɗin nasa, tare da gode masa bisa gudunmawar da ya bayar ga ƙasar nan tun bayan naɗin da aka yi masa a ranar 21 ga Agusta, 2023.
Onanuga ya ce Tinubu zai tura sunan wanda zai maye gurbin Badaru zuwa Majalisar Dattawa a cikin wannan makon.
Alhaji Badaru Abubakar, wanda ya kai shekara 63, ya riƙe muƙamin Gwamnan Jihar Jigawa na tsawon wa’adi biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin naɗin sa a matsayin Ministan Tsaro.







