Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Farfesa Jerry Gana, murnar cikar sa shekaru 80 da haihuwa, inda ya bayyana shi da “jagoran ƙasa na musamman, masani, kuma gwarzo mai kishin ƙasa.”
A cikin sanarwar da ya fitar yau, Idris ya ce: “Ina farin ciki ƙwarai wajen taya iyalai, abokai, abokan aiki, da masu yi mana fatan alheri a faɗin Nijeriya da wajen ta murna ga dattijon arziki na musamman, masani, kuma gwarzo mai kishin ƙasa, Farfesa Jerry Gana, a wannan biki na cikar sa shekara 80 a duniya, tare da ƙaddamar da sabon littafin tarihin rayuwar sa mai taken ‘Jerry Gana, Stewardship and Integrity’.”
Ya ce tarihin rayuwar Gana yana nuna zurfin sadaukarwa ga cigaban ƙasa, hidimar jama’a ta musamman, da tsare gaskiya ba tare da tangarɗa ba.
Ya ƙara da cewa: “Daga aji koyarwa a makaranta zuwa hawa babban matakin ƙasa da ya yi, ya nuna gagarumin jagoranci, zurfin basira, da kuma sadaukarwa mai ɗorewa ga haɗin kai da cigaban ƙasar mu.”

Idris ya ci gaba da cewa: “A matsayin sa tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Farfesa Gana ya shimfiɗa tubalan da har yanzu suke ci gaba da tsara fagen sadarwa da wayar da kan jama’a.
“Gudunmawar sa ga gina ƙasa, ƙarfafa dimokiraɗiyya, da ɗora al’umma kan haƙƙin ƙasa suna ci gaba da zama abin koyi ga tsararrakin sa shugabanni da ma’aikatan gwamnati.”
A cewar sa, ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon ministan ba wai taron murnar nasarar sa kaɗai ba ne, har ma wata muhimmiyar kafa ce ga masana, da masu tsara manufofi, da matasa ‘yan Nijeriya masu neman misalan jagoranci na gaskiya da riƙon amana.

Idris ya ce: “A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ina taya Farfesa Jerry Gana murnar kaiwa wannan gagarumin mataki.
“Ina addu’ar Allah ya ba shi lafiya mai ɗorewa, da ƙarfin jiki, da zaman lafiya na ganin amfanin hidimar sa ta rayuwa ga ƙasar mu.
“Ina taya ka murnar cika shekara tamanin, Farfesa Jerry Gana, ina taya ka murna kan wannan fitacciyar wallafa da aka yi.”







