• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Batutuwa 25 Dangane Da Manyan Attajirai 3,028 Na Duniya 

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 26, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0

 

* Tasirin Ɗangote da Abdussamad Rabi’u A Duniya

* Me Ya Sa Babu Ƙabilar Ibo A Jerin Attajiran Afrika Da Duniya Baki Ɗaya?

* Ɗangote: Bahaushen Da Mutum 82 Kaɗai Suka Fi Shi Ƙarfin Arziki A Duniya

*Abdussamad Rabi’u: Bahaushen Da Bayarabe Ɗaya Ne Ya Fi Shi Ƙarfin Arziki

Mujallar Forbes ta watan Afrilu, 2025 ta fito da sabon jadawalin attajiran duniya, su 3,028. A cikin bayanin da mujallar ta yi, ta bayyana cewa ta yi amfani da ma’aunin darajar Dalar Amurka a kasuwar hada-hadar canji ta ranar 7 ga Maris, 2025, inda ta auna ƙarfin arzikin kowanen su a Mizanin Hada-hadar Hannayen Jari a duniya.

New Citizen Hausa ta bi diddigin jadawalin waɗannan manyan attajirai su 3,025, inda ta zaƙulo waɗansu muhimman bayanai kamar haka:

1. Aliko Ɗangote shi ne mutum na 83 a jerin manyan attajirai na duniya, daga cikin mutum sama da biliyan 8 da miliyan 221 da ke raye a duniya, a ƙididdigar ranar 13 ga Maris, 2025.

2. Ɗangote shi ne baƙar fatan da ya fi kowane baƙar fata ƙarfin arziki a duniya.

3. Ƙarfin arzikin Ɗangote ya kai Dala biliyan 23.9, ko a ce Dala biliyan 24 a ƙiyasi.

4. Ɗangote shi ne mafi ƙarfin arziki a Afrika da Afrika ta Yamma.

5. Shekara 14 kenan a jere Ɗangote na riƙe da kambun mafi ƙarfin arziki a Afrika da cikin baƙaƙe na duniya bakiɗaya.

6. Ƙarfin arzikin Ɗangote ya nunka arzikin Yarabawa biyu masu ƙarfi a Afrika har sau uku da ɗoriya.

7. Abdussamad Rabi’u (BUA), shi ne na 3 a ƙarfin arziki a Najeriya, na 7 a jerin baƙaƙe na duniya, kuma na 6 na Afrika.

8. Ƙarfin arzikin Abdussamad BUA ya kai Dala biliyan 5.1 a ƙididdigar Forbes ta 2025.

9. Ɗangote ya ninka Abdussamad ƙarfin arziki har ninki huɗu.

10. Ƙididdigar Forbes dai na nufin babu wani ɗan ƙabilar Igbo ƙasaitaccen attajirin da ƙarfin arzikin sa ya kai ko ya haura darajar dala biliyan ɗaya.

11. Ƙididdigar ta nuna babu ɗan ƙabilar Igbo ko ɗaya a jerin manyan attajiran Afrika 20.

12. Wannan ƙididdiga ta nuna babu ɗan ƙabilar Igbo a jerin attajirai baƙar fata su 23 na duniya.

13. Attajirai huɗu ne kacal daga Najeriya waɗanda ke cikin jerin attajirai na duniya. Su ne Aliko Ɗangote, Mike Adenuga, Abdussamad Rabi’u da Femi Otedola. Wato Bahaushe biyu, Bayarabe biyu.

14. Ƙididdigar Forbes dai na nufin a ƙabilar Igbo babu mai ƙarfin arzikin mawaƙiyar nan ‘yar rawar kwambilo, wato Rihanna, wadda ke da Dala biliyan 1 da miliyan 400.

15. Daga cikin waɗannan attajirai 3,028 na duniya, 902 a Amurka suke. Sai Chana da Hong Kong 512. Indiya kuma 205.

16. A 1987, shekarar da Forbes ta fara wannan ƙididdigar, biloniyoyi 140 kaɗai aka samu a duniya. Bayan shekaru 20 kuma an samu biloniyoyi 1,000 a 2007.

17. Tsakanin 2007 zuwa 2017 adadin attajiran sun ƙaru zuwa mutum 2000.

18. Daga 2017 kuma zuwa 2025, adadin ya kai 3,028.

19. Cikin 2025 an samu ƙarin attajirai masu sama da Dala biliyan 1 har mutum 285 a duniya.

20. Ƙarfin arzikin Ɗangote ya kusa ninkawa ne a cikin 2025, albarkacin Matatar Ɗangote da ya gina a Legas.

21. A ƙididdigar 2024 ƙarfin arzikin Ɗangote ya na Dala biliyan 13.4 ne. An haɗa da matatar sa ce ya koma Dala biliyan 23.9 a 2025.

22. Elon Musk shi ne mafi ƙasaitar arziki a duniya, mai ƙarfin Dala biliyan 342.

23. Forbes ta jinjina wa Ɗangote wajen juriyar da ya nuna har ya gina katafariyar matatar man fetur, wadda ita ce ta bakwai a girma a duniya.

24. “Inda Ɗangote ya fi bada mamaki shi ne yadda ya kwashi tulin yashi daga cikin teku mai yawan ‘cubic’ miliyan 365, ya gina tashar jiragen ruwa tasa ta kan sa, don amfanin matatar sa,” cewar Forbes.

25. Ƙididdigar Forbes ta nuna ba a samun ƙasaitaccen attajiri a cikin manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati, sai dai a samu ƙasurgumin ɓarawo.

* Abin Lura: Duk dala biliyan 1 ta haura naira tiriliyan 1 da rabi.

Tags: AlikoDangoteattajiraiBUAForbesƙididdiga
Previous Post

Matsalar Tsaro A Katsina: Rayuwar Mazauna Yankunan Karkara Ƙarƙashin Yarjejeniyar Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Next Post

Batutuwa 25 dangane da attajirai 3,028 na duniya: Tasirin Ɗangote da Abdulsamad Rabi’u A Duniya

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post

Batutuwa 25 dangane da attajirai 3,028 na duniya: Tasirin Ɗangote da Abdulsamad Rabi'u A Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!