• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
February 2, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki, Rahoton Musamman
A A
0
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Tun sabuwar shekarar nan ta 2026 ba ta yi nisa ba, alamomi na ci gaba da nuna cewa tsare-tsaren ƙarfafa hadahadar kuɗaɗe, bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa farashi wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bijiro da shi zai samar da gagarumin cigaba.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da darajar Naira ke ƙara ƙarfi, inda a ƙarshen makon da ya gabata aka saida Dala ɗaya a ƙasa da Naira 1,400. A gefe ɗaya kuma farashin ɗanyen mai ya fara tashi, biyo bayan turnuƙun rikicin da ke neman mamaye yankin Gabas ta Tsakiya, dangane da rikici tsakanin Amurka da Iran a mashigin ruwa na Hormuz.

Hakan na nuni da cewa asusun ajiyar kuɗaɗen wajen Nijeriya ba da daɗewa ba zai ƙara cika maƙil, kamar yadda za a karanta a cikin wannan rahoto.

A yanzu tattalin arzikin Nijeriya na samun ƙarin ƙarfi sakamakon hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya, wanda ke ƙarfafa darajar naira tare da ƙara ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje.

A halin yanzu, farashin ɗanyen mai samfurin Brent yana kusan dala 69 kan kowace ganga, wanda ya fi kintace da hasashen ma’aunin kasafin kuɗin tarayya na shekarar 2026, na dala 64.85).

Wannan hauhawar farashin ɗanyen mai na ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati, yana ƙara cika asusun ajiyar kuɗaɗen waje, tare da taimakawa wajen daidaita darajar musayar kuɗi.

Masana na hasashen cewa idan rikici ya ɓarke sosai a Mashigin Hormuz—wurin da kashi 20 cikin 100 na jigilar man duniya ke wucewa—farashin ɗanyen mai samfurin Brent na iya tashi zuwa dala 91 ko ma dala 150 cikin ‘yan makonni.

Tunda darajar naira da asusun ajiyar kuɗaɗen waje sun riga sun fara ƙaruwa sakamakon muhimman gyare-gyare da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso ya aiwatar, wannan hauhawar farashin mai na iya ƙarfafa nasarorin da aka samu a makonni masu zuwa.

Farashin ɗanyen mai ya ƙaru a ranar Alhamis, inda ya ci gaba da tashi na kwanaki uku a jere, sakamakon fargabar cewa Amurka na iya ɗaukar matakin soja kan Iran, wanda ke daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da mai a Gabas ta Tsakiya.

Shi dai ɗanyen mai samfurin Brent ya tashi da senti 94 (kashi 1.4%) zuwa dala 69.34 a kowace ganga, yayin da man WTI na Amurka ya tashi da kashi 1.5% zuwa dala 64.13.

Babban abin da ke haddasa hauhawar farashin shi ne barazanar siyasa da tsaro da ta shafi Iran da Gabas ta Tsakiya, tare da katsewar samar da mai ba tare da tsari ba a Kazakhstan da Amurka.

Masana sun ce barazanar rikicin Amurka da Iran, takunkumin Amurka kan ɗanyen man Rasha, da kuma ci gaba da buƙatar mai daga Chana na iya sa farashin mai ya ci gaba da kasancewa a sama, duk da cewa kasuwanni sun shiga shekarar nan ta 2026 da tsammanin samar da yawan ɗanyen mai fiye da wanda buƙata.

A ɓangaren Nijeriya, hauhawar farashin mai na da matuƙar muhimmanci saboda fiye da kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na ƙasar na fitowa ne daga mai.

Wannan yana taimakawa wajen ƙarfafa tattalin arziki da samun daidaito.

A halin yanzu, darajar Dala ta sauka ƙasa, inda farashin ta ya sauka zuwa ƙasa da naira N1,400 kan dala ɗaya a kasuwar hukuma karon farko cikin sama da shekara guda.

Bayanai daga CBN sun nuna cewa farashin musayar kuɗi a Kasuwar Musayar Kuɗi ta Nijeriya (NFEM) ya inganta zuwa N1,396.99/$ daga N1,400.48/$ a ranar Laraba.

A kasuwar ‘yan canji, naira ma ta ƙara ƙarfi, inda ta inganta zuwa N1,454/$, bisa bayanan Cowry Asset Management Limited, wanda ke nuna kyakkyawan yanayi a dukkan kasuwannin kuɗi.

Shugaban Ƙungiyar Masu Canjin Kuɗi (ABCON), Aminu Gwadabe, ya ce naira ta samu tagomashi na tsawon watanni, abin da ya kawo ƙarshen shekaru na rincaɓewar kasuwa.

Daraktan Kamfanin Financial Derivatives Company, Bismarck Rewane, ya ce a bisa tsarin ƙimar sayen kuɗi (PPP), ainihin darajar naira na kusa da N1,257/$, yana mai cewa naira na ƙarƙashin darajar ta da kusan kashi 11%.

Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Waje na Nijeriya ma na ci gaba da ƙaruwa, inda ya kai dala biliyan 46.11 zuwa ranar 28 ga Janairu 2026, daga dala biliyan 40.29 a Disamba 2024. Wannan shi ne karo na farko cikin kusan shekaru takwas da asusun ajiyar ya wuce dala biliyan 46.

Masana sun ce wannan ƙaruwa na nuna ƙarfin tattalin arziki, ingantaccen kula da kasuwar kuɗi, da dawowar amannar amincewa da masu zuba jari suka yi wa Nijeriya.

Shigowar jarin ƙasashen waje ya kai dala biliyan 20.98 cikin watanni 10 na shekarar 2025, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 70% idan aka kwatanta da shekarar 2024, da kuma kashi 428% idan aka kwatanta da 2023.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce naira yanzu tana fuskantar hadahada bisa turbar sauye-sauye, inda bambancin da ke tsakanin kasuwar hukuma da ta ‘yan canjin game-gari ya ragu zuwa ƙasa da kashi 2%, daga sama da kashi 60% a baya.

Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗi na ƙaruwa ne ba ta hanyar rance ba, sai dai ta hanyar ingantaccen aiki na kasuwa, ƙarin fitar da kayayyaki ba na ɗanyen mai ba, da shigowar jari.

Farfaɗo da manufofi masu muhimmanci kamar cire tallafin fetur, gyaran haraji, ƙarfafa jarin bankuna, da inganta haɗin gwiwar manufofin kuɗi da na kasafin kuɗi, sun taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

A ƙarshe, rahoton NNPC Ltd ya nuna cewa kuɗaɗen shigar kamfanin sun kai naira tiriliyan 5.08 a watan Oktoba 2025, yayin da ribar bayan biyan haraji ta kai Naira biliyan 447. Hakan ke nuna ingantaccen aiki da farfaɗowar samar da ɗanyen mai da gas, a lokacin da ita ma naira take ci gaba da kankaro darajar ta kasuwar musayar kuɗaɗen waje.

* Barkiya mai sharhi ne kan al’amurran tattalin arziki, tsaro da siyasa

Tags: CBNOlayemiCardoso
Previous Post

Sojoji sun karkashe ɗimbin ’yan bindiga a dajin Zamfara

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan Nijeriya miliyan 10 kan hadahadar kuɗi

Related Posts

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa

May 3, 2026
Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda

May 1, 2026
Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna

May 1, 2026
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Juyin Zamani: Yadda CBN ke ƙarfafa wa ɗalibai koyon ilmin sarrafa kuɗi, yayin da tattalin arziki ke sauyawa a zamanance 

April 30, 2026
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

April 29, 2026
Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna

April 27, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan Nijeriya miliyan 10 kan hadahadar kuɗi

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin horar da ’yan Nijeriya miliyan 10 kan hadahadar kuɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!