• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Kwankwaso ya ce a shirye yake ya shiga APC, amma ya gindaya sharuɗɗa 

Mun taɓa taimakawa aka ci yaƙi amma aka bar mu da kuturun doki, inji shi

ALI KANO by ALI KANO
January 15, 2026
in Siyasa
A A
0
Kwankwaso ya ce a shirye yake ya shiga APC, amma ya gindaya sharuɗɗa 
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso A wani taron siyasa a shekarun baya

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso A wani taron siyasa a shekarun baya

Jagoran jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa bai ƙi shiga jam’iyyar APC ba, sai dai yana taka-tsantsan ne sakamakon abubuwan da suka faru a baya.

Kwankwaso ya faɗi hakan ne yayin da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya da magoya bayan sa daga Rano da Dawakin Tofa a gidan sa da ke Kano a ranar Laraba, inda ya ce an yi kuskuren fahimtar matsayin sa.

Ya ce: “Ban ce ba zan shiga APC ba, amma dole ne a fara ba mu cikakken tabbaci game da makomar gwamnatin Jihar Kano kafin mu shiga APC.

“Mecece makomar ‘yan majalisun mu da sauran magoya bayan mu kafin mu amince mu sauya sheƙa?”

Tsohon gwamnan ya tuna da wasu haɗin gwiwar siyasa da aka yi a baya inda ɓangaren sa ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnatoci, amma daga bisani aka ci yaƙi aka bar su da kuturun doki.

Kwankwaso ya jaddada cewa duk wani sauya sheƙa da za a yi dole ne ya kasance bisa ga tabbatattun alƙawurra masu bayyana kariyar magoya bayan sa da tsarin gwamnatin Jihar Kano.

Ya kuma nanata cewa babu wata cikakken garanti da aka bayar har yanzu don kare muradun Kwankwasiyya ko tabbatar da adalci ga membobin ta a duk wata sabuwar haɗaka.

“Ba tare da rubutattun tabbaci ba, barin NNPP zai kasance gaggawa kuma abu mai haɗari,” inji shi.

Kwankwaso ya sake jaddada ƙudirin sa na kare amana da muradun magoya bayan sa, yana mai tabbatar masu da cewa ba za a ɗauki kowace irin shawara ba tare da tattaunawa mai faɗi da kuma tabbacin amfanin al’umma ba.

Tags: APCKanoNNPPRabi'uKwankwasosauyasheƙa
Previous Post

Sarkin Kano Sanusi ya koma jami’a, ya yi rajista don karatun digirin Shari’a

Next Post

Ilimin ‘ya mace: Fiye da ‘yan mata 40,000 a Kaduna sun amfana da shirin koyon dabarun rayuwa na Gwamna Uba Sani

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Ilimin ‘ya mace: Fiye da ‘yan mata 40,000 a Kaduna sun amfana da shirin koyon dabarun rayuwa na Gwamna Uba Sani

Ilimin ‘ya mace: Fiye da ‘yan mata 40,000 a Kaduna sun amfana da shirin koyon dabarun rayuwa na Gwamna Uba Sani

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!