• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Matsalar tsaron Nijeriya tana hana ni barci, inji Tinubu a taron cikar ACF shekaru 25

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 22, 2025
in Labarai
A A
0
Matsalar tsaron Nijeriya tana hana ni barci, inji Tinubu a taron cikar ACF shekaru 25
Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, yana gabatar da jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum, ACF) shekaru 25 da kuma ƙaddamar da Asusun Tallafin ta... a Kaduna a ranar Juma'a

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, yana gabatar da jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum, ACF) shekaru 25 da kuma ƙaddamar da Asusun Tallafin ta... a Kaduna a ranar Juma'a

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wata babbar damuwa da ke tasiri a zuciyar sa fiye da matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Nijeriya, musamman tashin hankalin da ya addabi sassa da dama a Arewa.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum, ACF) shekaru 25 da kuma ƙaddamar da Asusun Tallafin ta.

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, shi ne ya wakilci Tinubu a wajen taron wanda aka yi a Ɗakin Taro na Umaru Musa Yar’Adua.

Shugaban Ƙasa ya bayyana matsalar tsaro a matsayin barazana mafi tsanani da ƙasar nan take fuskanta, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba za ta iya komawa kan turbar farfaɗowar tattalin arziki ko zaman lafiyar al’umma ba muddin ba a dawo da zaman lafiya ba.

“Babu abin da ke damu na sosai fiye da matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya, musamman Arewacin Nijeriya,” inji shugaban.

Ya ƙara da cewa, “Ba za mu ci gaba ba idan wani ɓangare na jikin ƙasa ya tsaya cik.”

Ya ce gwamnatin sa ta gaji yanayin tsaro mai rikitarwa ne wanda ya haɗa daga ta’addanci zuwa ta’addancin ’yan fashi da garkuwa da mutane, amma tana fuskantar matsalar da gaggawa, da jajircewa da kuma bin sababbin tsare-tsaren gyara.

Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar kawar da ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke addabar Arewa tare da dawo da ƙarfin tattalin arzikin yankin da rikice-rikice suka daɗe suna durƙusarwa.

Barau Jibrin, Tajuddeen Abbas, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, a taron

Ya bayyana cewa gina amana tsakanin al’umma, ƙarfafa haɗin kai da dawo da tsaro matakai ne da dole a ɗauka domin hana rikicin ya ƙara lalacewa, musamman a ɓangaren ilimi da noma.

Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Tinubu ya nuna ƙwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin Arewa.

Ya ce yana fatan ganin lokacin da manyan motoci masu ɗaukar ɗanyen man fetur za su fara fita daga Kolmani da sauran sababbin wuraren haƙar mai na Arewa, alamar sababbin damar masana’antu da ƙaruwar kuɗaɗen shiga.

Ya ƙara da cewa manyan ayyukan gine-gine, ciki har da babban titin Abuja–Kaduna–Kano, ana hanzarta aikin su domin kammala su don bunƙasa zirga-zirga, cinikayya da haɗe yankuna.

Tinubu ya ce dole Arewa ta fuskanci matsalolin ta da gaskiya, jarumta da jagoranci mai haɗe kai.

“Mun gaza samun ranar da muke yin barci cikin kwanciyar hankali alhali miliyoyi suna kwanciya da yunwa, ranar da tsoro ya zama abokin tafiya na dindindin ga matafiya,” inji shi.

Ya nuna cewa shekaru da dama na tangal-tangal sun raunana haɗin kai, amma bambance-bambancen jama’ar da aka gani a bikin cikar ACF shekaru 25 alama ce ta sabuwar aniyar ƙin rarrabuwa da dawo da zumunci.

Shugaban ya yaba wa ACF bisa kasancewa “lamirin Arewacin Nijeriya” a tsawon shekaru 25 da suka gabata.

Ya ce zagayowar bikin murnar shekarun ta nuna shekaru na jarumtaka, kare gaskiya da hidimta wa al’umma wajen kare mutunci, adalci da daidaito ga miliyoyin ’yan Arewa.

Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa, gargajiya, al’umma da addini da su sake dagewa wajen kiyaye manufofin da suka sa aka kafa ACF, yana mai jaddada cewa zaman lafiyar Arewa muhimmin ginshiƙi ne ga zaman lafiya da cigaban Nijeriya baki ɗaya.

Tags: Arewa Consultative Forum (ACF)bikin cikar shekaruKadunaShugaban Ƙasa Bola Ahmed TinubuTajuddeen AbbastsaroƘungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF)
Previous Post

Hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu ya ƙara dagula matsalolin Nijeriya, inji Peter Obi

Next Post

Kwamandan soji ya umurci dakaru da “bin diddigin masu garkuwa ba tare da gajiyawa ba” domin ceto ɗaliban Neja da aka sace

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Kwamandan soji ya umurci dakaru da “bin diddigin masu garkuwa ba tare da gajiyawa ba” domin ceto ɗaliban Neja da aka sace

Kwamandan soji ya umurci dakaru da “bin diddigin masu garkuwa ba tare da gajiyawa ba” domin ceto ɗaliban Neja da aka sace

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!