• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Kisan gilla a Borgu: ’Yan bindiga sun kashe mutum 42, sun sace da dama a Jihar Neja

ALI KANO by ALI KANO
January 4, 2026
in Tsaro
A A
0
Kisan gilla a Borgu: ’Yan bindiga sun kashe mutum 42, sun sace da dama a Jihar Neja
Wani sashe na kisan gillar

Wani sashe na kisan gillar

Aƙalla mutane 42 ne aka kashe, yayin da aka sace wasu da dama—har da yara ’yan makaranta—biyo bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da aka kai wa al’ummomi a ƙananan hukumomin Agwara da Borgu na Jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce hare-haren, da suka ɗauki sama da mako guda suna gudana, sun faru ne ba tare da wani gagarumin turjiya ba sakamakon rashin jami’an tsaro a wuraren da abin ya shafa.

A cewar majiyar, “Sun ɗaure hannayen mutane 37 a baya sannan suka yanka su a Kasuwar Daji kusa da Papiri, yayin da aka kashe wasu biyar a ƙauyen Kaima.

“Sun kuma sace mutane da dama, ciki har da yara, wasu daga cikin su ɗalibai ne na Makarantun Katolika masu zaman kan su na Firamare da Sakandaren St. Mary’s da ke Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara.

“Gwamnati da hukumomin tsaro su zo su taimake mu. Muna fuskantar babbar matsala a can bayan kogi inda aka tafi da waɗannan ɗalibai,” inji majiyar.

Mazauna yankin sun ƙara da bayyana cewa an banka wa kasuwar gari wuta a ranar Asabar, an kwashe kayayyaki daga shaguna tare da satar kayan abinci, sannan aka sake sace ƙarin mutanen ƙauyuka, ciki har da yara.

Da yake tabbatar da harin da aka kai wa ofishin mishan na Katolika, Daraktan Sadarwa na Diocese na Katolika na Kontagora, Rev. Father Stephen Kabirat, ya ce maharan sun kuma lalata kadarorin coci yayin harin.

“Faston mu na cocin yankin ya tsallake rijiya da baya daga sacewa, lokacin da maharan suka zo gidan mishan kwanaki uku da suka wuce,” inji Kabirat.

Ya ce: “Sun lalata wasu sassan coci, sun tafi da babura guda biyu da kuɗi sama da ₦200,000, sannan suka sace wasu mazauna gari, ciki har da yara.”

Wani mazaunin yankin da ya roƙi hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa, ya ce tsoro ya tilasta wa al’ummomi barin muhallan su.

“Yanzu haka, mutanen wasu daga cikin ƙauyukan da aka sace yaran makaranta daga cikin su suna kwana a daji bayan sun koma gida, saboda tsoron sake kai musu hari,” inji mazaunin.

A halin da ake ciki, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ta tabbatar da hare-haren. A cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda, SP Wasiu Abiodun, ya ce rundunar ta samu rahoton mamayar ’yan bindiga makisa a daren Asabar.

“Da misalin ƙarfe 9:00 na dare, ’yan sanda sun samu bayani cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kan al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Borgu, inda suka kashe sama da mutane 30 tare da sace wasu da ba a tabbatar da adadin su ba,” inji sanarwar.

Abiodun ya bayyana cewa tun da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ranar, ’yan bindigar da ake zargin sun fito daga Dajin National Park na yankin Kabe, sun kai hari Kasuwar Daji a ƙauyen Demo, inda suka kashe jama’a, suka ƙona kasuwa, tare da kwashe kayayyaki daga shaguna.

Ya ƙara da cewa rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta kai ziyara wuraren da abin ya shafa, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace tare da dawo da zaman lafiya.

“Za a ba da sanarwar ƙarin bayani idan an samu,” inji kakakin ’yan sanda.

Tags: 'yan bindiga'yan sanda'yan ta'addaAgwaraBorguharimaharaNejarashin tsarota'addanci
Previous Post

Kotu ta sake tsare Malami, ɗan sa da matar sa a Gidan Gyaran Hali na Kuje

Next Post

Muhimmin lokaci a Nijeriya: Hujjar da ta sa hanyar da aka ɗauka ita ce mai ɓullewa

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Tinubu ya sha alwashin ganin bayan maƙiyan Nijeriya, ya girmama marigayi Abubakar Audu

Muhimmin lokaci a Nijeriya: Hujjar da ta sa hanyar da aka ɗauka ita ce mai ɓullewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!