• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Nishaɗi Da Al'adu

Iyaye ku koyar da yara muhimmancin karatu da rubutu – Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja

MUKHTAR YAKUBU by MUKHTAR YAKUBU
December 8, 2025
in Nishaɗi Da Al'adu
A A
0
Iyaye ku koyar da yara muhimmancin karatu da rubutu – Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja
Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano, Hajiya Sa'adatu Salisu Yusha'u Soja

Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano, Hajiya Sa'adatu Salisu Yusha'u Soja

AN yi kira ga iyaye da su tashi tsaye wajen koyar da yaran su tare da nuna musu muhimmancin karatu da rubutu a harshen Hausa domin su tashi da kyawawan halaye da al’adu na iyaye da kakanni.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja, a lokacin da take jawabi a taron ƙaddamar da littattafan ‘Abokiyar Zama’ da ‘Lokaci’, waɗanda Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya ta rubuta, a shekaranjiya Asabar a ɗakin taro na Mahmoud Tukur da ke tsohuwar Jami’ar Bayero da ke Kano.

Hajiya Sa’adatu ta ce: “A wannan lokaci da aka samu gurɓatar al’amuran rayuwa, yana da matukar muhimmanci a ɗora yara masu tasowa a hanyar nuna musu muhimmancin karatu da rubutu domin su tashi da halaye nagari kamar yadda muka gada a wajen iyayen mu.

“Abu ne mai muhimmancin gaske a cusa al’adu, don ta haka ne za a samu yara na gaba masu tarbiyya da kuma kishin kan su.”

Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja

Ta ci gaba da cewa, “Ni na tashi a ƙauye, don haka ni rayuwar ƙauye na yi, kuma ni a karatu na ba siyasa na karanta ba, amma a yanzu na samu kai na a cikin siyasa a matsayin Shugabar Ƙaramar Hukuma, don haka a yanzu ina ganin matsaloli da dama, musamman ta fuskar zamantakewar aure da kuma rayuwar yara mata kafin a yi musu aure.

“Wannan ya sa a yanzu na duƙufa wajen rubuta littafi duk da ba ni da wadataccen lokaci, amma na kan yi rubutun na tura shi ga malami na yana dubawa tare da gyara mini ta yadda nan gaba idan ya kammala za a buga shi domin amfanin jama’a.

“Kuma na ji daɗi da nake samun damar yin rubutun domin fito da wasu matsalolin da suke damun mu ta fuskar zamantakewar rayuwa, musamman mata wanda nake tunanin zai amfani jama’a idan littafin ya fito, ina fatan samun ƙwarin gwiwa daga gare ku domin ganin wannan littafin ya kammala, domin aiki ne na jama’a gaba ɗaya, ba nawa ni kaɗai ba.”

Hajiya Sa’adatu tana gabatar da jawabi a taron

A ɓangaren marubuta kuwa, kira ta yi ga marubuta da su tashi tsaye wajen bincike domin gano matsalolin da suke damun al’umma domin yin rubutu a kan su, don a wayar da kan matasa abin da ya kamata su yi mai kyau da kuma abin da ya kamata su nesanta domin rashin kayan sa.

“Ina ƙarfafa wa matasa, musamman mata, su dage da karatu da rubutu har ya zama ɗabi’ar su ta yadda za su yaƙi jahilci da munana ɗabi’u.”

Previous Post

Amfani da ‘yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso

Next Post

Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje

Related Posts

Yadda Mama Nike ta tsaya da ƙafar ta bayan kuɓuta daga gallazawar miji
Nishaɗi Da Al'adu

Yadda Mama Nike ta tsaya da ƙafar ta bayan kuɓuta daga gallazawar miji

May 30, 2026
Hausa da Hausawa a Ghana
Nishaɗi Da Al'adu

Hausa da Hausawa a Ghana

May 23, 2026
Cewar Shugaba Tinubu: Bikin Argungu shaida ce ta dawowar zaman lafiya, na yi alƙawarin goyon baya ga noma da yawon buɗe ido
Nishaɗi Da Al'adu

Cewar Shugaba Tinubu: Bikin Argungu shaida ce ta dawowar zaman lafiya, na yi alƙawarin goyon baya ga noma da yawon buɗe ido

February 14, 2026
Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha
Mahanga

Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha

February 13, 2026
Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya
Nishaɗi Da Al'adu

Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya

January 21, 2026
Next Post
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje

Kamfanonin 'yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!