• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Amfani da ‘yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso

ALI KANO by ALI KANO
December 8, 2025
in Tsaro
A A
0
Amfani da ‘yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso
Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso

Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon Ministan Tsaro, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi gargaɗin cewa barin gwamnonin jihohi su kafa kuma su yi amfani da rundunonin ‘yan sa-kai “marasa isasshen horo na ƙwararru” zai ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai da manyan makamai cikin sauƙi a faɗin ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa ga manema labarai, Kwankwaso ya ce amincewar Gwamnatin Tarayya da wannan mataki, ko da kuwa an yi shi da kyakkyawar niyya ne, ya riga ya ƙarfafa wasu mutane su fara kafa nasu rundunar tsaro nasu na kan su, wanda hakan ke ƙara barazana ga zaman lafiyar da ake ciki.

Ya ce: “Abubuwan da ke faruwa kwanan nan a ƙasar mu sun cika ni da damuwa matuƙa game da halin da al’amuran ƙasar mu ke ciki.

“Ni da na yi aiki a cikin tsarin a tsawon shekaru, na san cewa babban nauyin yaƙi da rashin tsaro a Nijeriya ya rataya ne a wuyan Gwamnatin Tarayya tare da haɗin kai da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.

“Abin takaici, kamar Gwamnatin Tarayya ta kasa shawo kan lamarin.

“Hakan ya bayyana a yadda ta amince da barin jihohi su kafa su kuma tura rundunonin ‘yan sa-kai ba tare da horon ƙwararru ba.

“Wannan mataki, ko da an yi shi da niyya mai kyau, yana haifar da yawaitar ƙananan makamai da manyan makamai ba tare da kulawa ba a faɗin ƙasar nan.

“Abin da ya fi muni ma, wasu mutane sun fara amfani da wannan damar wajen kafa nasu dakarun tsaron, kamar yadda ake gani daga wasu ‘yan siyasa. Wannan yana ƙara barazana ga zaman lafiyar ƙasar mu.”

Jagoran na rundunar siyasa ta Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano ya ƙara da cewa: “Wani abin damuwar kuma shi ne yadda ake ƙara yawan nuna bambancin ƙabilanci da na yanki ga ‘yan Nijeriya a ƙasar su. A ‘yan kwanakin nan mun ga rahotanni masu tayar da hankali na yadda ake kama mutane – musamman daga wani yanki – ba bisa ƙa’ida ba, ana tsare su, ana cin zarafin su, a wasu lokuta ma ana azabtar da su a wasu sassan ƙasar nan.

“Hakan ya ƙara muni saboda yaɗa tsangwama, barazana da kalaman ƙiyayya a kafofin sada zumunta, wanda sau da yawa ake tunzura shi saboda son zuciya na ƙabilanci da addini. Waɗannan abubuwa barazana ce mai girma ga haɗin kan ƙasa.”

Ya kira Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin daƙile “waɗannan abubuwa masu haɗari kafin su ƙara fita daga hanya.”

Ya ce: “A matsayi na na tsohon Ministan Tsaro kuma Shugaban Kwamitin Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai da Manyan Makamai, abin yana ba ni tsoro matuƙa ganin yadda ake yawo da makamai cikin sauƙi a ƙasar nan — wanda bai dace ba.”

Kwankwaso ya taya Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) murnar samun “naɗin da ya dace da shi ƙwarai” a matsayin Ministan Tsaro.

Ya ce: “Ina da yaƙinin cewa, idan akwai cikakken ƙwarin gwiwar siyasa da goyon baya, yana da ƙwarewar da da ake buƙata wajen taka rawar gani domin dawo da tsaro da kwanciyar hankali ga ƙasar mu.”

Tags: 'yan sa-kaigargaɗiKwankwasomakamaitsaro
Previous Post

Tinubu ya yabi sojojin Nijeriya kan kare dimokiraɗiyya a Benin

Next Post

Iyaye ku koyar da yara muhimmancin karatu da rubutu – Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Iyaye ku koyar da yara muhimmancin karatu da rubutu – Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja

Iyaye ku koyar da yara muhimmancin karatu da rubutu - Sa'adatu Salisu Yusha'u Soja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!