MARIGAYIYA HAJIYA AMINA (GWAGGON KANO), MATAR SIR AHMADU BELLO, GCON, KBE, SARDAUNAN SAKKWATO, FIRIMIYAN JIHAR AREWA NA FARKO KUMA NA ƘARSHE
‘Yar Sarkin Bichi Abubakar ce, shi kuma Sarkin Bichi Abubakar ɗan Sarkin Bichi Mustapha ne. An haife ta a garin Bichi a shekarar 1923.
Ta fara karatun addinin Musulunci tun tana da misalin shekaru 3 zuwa 4, ta kuma shiga Makarantar Elementare ta Bichi a lokacin da ta kai kimanin shekaru 7. Tana a Makarantar Midil sai aka aurar da ita ga mijin ta, watau Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato), ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu, ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II/Mai Raɓah, ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo tagammadahullah bi rahamatihi.
Hajiya Amina Gwaggon Kano ce ta haifa wa Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello ‘ya’yan sa guda uku, wato Hajiya Fatima (wadda Shata ya yi wa waƙar ‘Hajiya Inno Ɗiyar Ahmadu’) da Hajiya A’isha da kuma Hajiya Luba; duk da yake akwai ɗa namiji da ta haifa bayan haihuwar Hajiya Inno, kafin ta haifi Hajiya A’isha, ya rasu ne tun yana jinjiri.
Hajiya Fatima (‘Hajiya Inno Ɗiyar Ahmadu’) ta auri mai girma Wamban Kano, Alhaji Abubakar (Habu Ɗan Maje) ɗan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, ɗan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, ɗan Sarkin Kano Malam Abbas, ɗan Sarkin Kano Malam Abdullahi Maje Karofi, ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo.
Hajiya A’isha ta auri mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba, ɗan Magajin Garin Sakkwato Usman wanda tsatso ne daga Magajin Garin Sakkwato na farko, Malam Abubakar Ɗan Jada da aka fara naɗawa Magajin Garin cibiyar Daular Usmaniyya a cikin shekarar 1817.
Hajiya Luba kuma ta auri Mai Girma Marafan Sakkwato, Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi, ɗan Alhaji Aliyu Bisije, ɗan Dagacin Gasma Muhamman (a Ƙaramar Hukumar Mulkin Karasuwa ta Jihar Yobe).
Waɗannan ‘ya’ya da Hajiya Amina Gwaggon Kano ta haifa sun haifa mata jikoki da tattataɓa-kunne da dama. Misali, Hajiya Fatima (‘Hajiya Inno Ɗiyar Ahmadu’) ita ce ta haifi Hajiya Hadiza wadda ta auri tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato (jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara na yau), Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa (Turakin Argungu/Turakin Kabi na farko).
Hajiya A’isha ce ta haifi Hajiya Asma’u, uwargidan Mai Girma Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami, da Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmad Ɗanbaba, da sauran su.
Hajiya Luba kuma ta haifi Hafsatu da Ahmadu da ake yi wa kinaya da Sardauna.
Daga cikin waɗannan ‘ya’ya nata, Hajiya Luba ce ke raye. Kenan Allah ya karɓi ran Hajiya Fatima (‘Hajiya Inno Ɗiyar Ahmadu’) da kuma Hajiya A’isha.
A yayin da Dakta Mamman Shata Katsina ya yi wa biyu daga cikin waɗannan ‘ya’ya uku da Gwaggon Kano ta haifa waƙa, wato ‘Hajiya Inno Ɗiyar Ahmadu’ da ‘Luba ‘Yar Sarkin Sudan Bello’, shi kuma Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a waƙar da ya yi wa mahaifin su, Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) mai amshi ‘Ya Wuce Reni Ba A Yi Mai Shi, Ahmadu Jikan Garba Sadauki’, ya jero su ne yana cewa: “Mai girma ɗan mai girma, uban Luba baban A’i da Inno…”
Allah ya karɓi rayuwar Hajiya Amina Sir Ahmadu Bello (Gwaggon Kano) a garin Sakkwato a ranar 27/06/2004.
Allah ya jaddada rahama zuwa ga magabatan mu duka, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
* Alhaji Ibrahim Muhammad shi ne Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya
Tarho: 08149388452,
08027484815.
Imel: birninbagaji4040@gmail.com






