• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gaggauta Bayar Da Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Manoma

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 11, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya Za Ta Gaggauta Bayar Da Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Manoma
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a taron

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a taron

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayar da umarnin a gaggauta sakin lamunin naira biliyan 250 ga ƙananan manoma a faɗin Nijeriya.

Umarnin, wanda aka bai wa Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Fadar Shugaban Ƙasa (PFSCU), yana zuwa ne da nufin hanzarta rabon bashin wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi don bunƙasa noman rani a yayin da ake tsakiyar damina don tabbatar da ci gaba da samar da wadataccen abinci ba tare da ƙaƙƙautawa ba

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya gargaɗi hukumar da cewa dole ta gaggauta samar da tsarin aiwatar da rabon lamunin ta inda Kuɗaɗen za su kai ga manoman da abin ya shafa ba tare da jan ƙafa ba, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci gafara-sa ba ta ga ƙaho ba.

A cewar sa, “Gwamnatin Shugaba Tinubu ta samar da shirin ne don ganin ‘yan Nijeriya sun amfana a kan lokaci ba don ajiyar kuɗaɗe ba.”

Shettima, wanda ya yaba wa irin gudunmawar da Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar PFSCU don yin gyaran fuska ga tsare-tsaren samar da abinci ba tare da tarnaƙi ba, musamman a ɓangaren sassauta hanyoyin samar da kayan haɗa taki da kafa asusun tallafin Shugaban Ƙasa, ya ƙara da cewa, “Idan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, hukumomi da masana’antu masu zaman kan su za su haɗa kai, ƙudirin gwamnati zai samar da ayyukan cigaban ƙasa na zahiri cikin ƙanƙanen lokaci.”

Tuni dai gwamnoni da masu ruwa da tsaki da suka sami halartar taron suka yaba da wannan matsayar da gwamnatin ta ɗauka, inda suka ce za su bayar da duk wani goyon baya ga kwamitin shugaban ƙasar don ganin an samar da tsari mai kyau wajen rabon tallafin.

Tags: Kashim ShettimalamunimanomaPFSCU
Previous Post

Tsohon Shugaban NNPCL, Kyari ya Kwana Hannun EFCC Yana Amsa Tambayoyi

Next Post

Gwamnatin Kano Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Hassana Da Hussaina, Tagwayen Da Aka Haifa Manne Da Juna

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Gwamnatin Kano Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Hassana Da Hussaina, Tagwayen Da Aka Haifa Manne Da Juna

Gwamnatin Kano Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Hassana Da Hussaina, Tagwayen Da Aka Haifa Manne Da Juna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!