• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Hassana Da Hussaina, Tagwayen Da Aka Haifa Manne Da Juna

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 12, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Kano Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Hassana Da Hussaina, Tagwayen Da Aka Haifa Manne Da Juna
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ɗauke da ɗaya daga cikin jariran, tare da iyayen su da jami'an gwamnati

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ɗauke da ɗaya daga cikin jariran, tare da iyayen su da jami'an gwamnati

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta ɗauki nauyin karatun ‘yan tagwayen jihar waɗanda aka haifa a manne, bayan da ƙasar Saudiyya ta yi nasarar kammala aikin raba su.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya tarbi tagwayen a filin jirage na Malam Aminu Kano, bayan da hukumar Saudiyya ta dawo da su gida Kano.

Gwamnan ya ce gwamnatin sa za ta ɗauki nauyin karatun su har zuwa jami’a, tare da ci gaba da kula da ɗawainiyar lafiyar su da ta iyayen su.

Yusuf ya ce gwamnati za ta samar da wani tsari da zai tabbatar da ɗorewar kula da tagwayen ko da bayan kammala gwamnatin sa.

Gwamna Yusuf da jami’an Saudiyya tare da tagwayen a filin jirgin sama a Kano

Ya gode wa Gidauniyar Sarki Salman bin Abdul’aziz da Ofishin Jakadancin Saudiyya bisa ɗaukar nauyin gudanar da aikin raba tagwayen.

Da yake jawabin godiya, mahaifin tagwayen, Malam Hassan Isah, ya gode wa Saudiyya bisa aikin da aka yi masu kyauta da kuma kyakkyawar kulawar da aka ba su a yayin zaman su a ƙasa mai tsarki tsawon shekaru biyu.

Kazalika ya gode wa gwamnan Kano bisa kyakkyawan jagorancin sa da bibiya domin tabbatar da an yi aikin cikin nasara.

A cikin Oktoba 2023 ne Saudiyya ta ɗauki nauyin aikin raba ‘yan tagwayen mata, Hassana da Hussaina, waɗanda aka haifa a manne, inda suka shafe tsawon shekaru biyu a ƙasar ana kula da lafiyar su, bayan an kammala aikin tiyatar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi a lokacin da ya tarbi jariran da iyayen su
Gwamna Yusuf ɗauke da ɗaya daga cikin tagwayen
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gaggauta Bayar Da Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Manoma

Next Post

Tinubu ya ƙaddamar da shirin kula da lafiyar mata don rage mace-macen mata masu juna biyu

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Tinubu ya ƙaddamar da shirin kula da lafiyar mata don rage mace-macen mata masu juna biyu

Tinubu ya ƙaddamar da shirin kula da lafiyar mata don rage mace-macen mata masu juna biyu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!