Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da shirin horas da ’yan Nijeriya miliyan 10 kyauta kan ilimin hadahadar kuɗi da shigar kuɗi cikin tsari, inda ta ce matasa da mata ne ginshiƙin cin gajiyar yawan al’ummar ƙasar nan.
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, shi ne ya bayyana hakan yau a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja yayin da yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ba za a iya gina tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ba tare da ƙwararrun ma’aikata, nagartattun ƙa’idoji da ingantaccen tsarin sana’o’i ba.
A yayin taron, Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, ta hannun Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Hadahadar Kuɗi da Tattalin Arziki (PreCEFI), ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da manyan ƙungiyoyin ƙwararru shida da suka haɗa hada da ICAN, CIBN, CIS, NICA, CRMI da NIIE.
Yarjejeniyar na da nufin tsara horo, bada takardar shaidar ƙwarewa, amfani da fasahar zamani da tsarin tallafi domin ƙarfafa gwiwar ’yan kasuwa, musamman mata da matasa.
Shettima ya ce hadahadar kuɗi ba ta tsaya ga samun dama kaɗai ba, sai an samu ilimi, ƙwarewa da amana.
Shugaban ICAN, Malam Haruna Nma Yahaya, ya yaba wa gwamnatin Tinubu bisa gyare-gyaren tattalin arziki da suka haifar da ƙaddamar da shirin.
Ya tabbatar da cikakken goyon bayan ƙungiyoyin ƙwararru wajen ganin an cimma nasarar shirin.
Haka nan, Shugaban WAWU Africa, Emmanuel Lennox, ya ce sun shirya samar da dandamalin zamani da kayan aiki da za su tabbatar da ingancin horon.
An bayyana cewa shirin na da muhimmanci domin rage ficewar jama’a daga tsarin hadahadar kuɗi sakamakon ƙarancin ilimi da ƙwarewa.







