• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 29, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata wani bauɗaɗɗen rahoton da aka ce ya sayar wa manyan dillalan mai har dalar Amurka biliyan 1.259 domin su shigo da fetur da dangogin sa daga waje.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai ta CBN kuma Daraktar Riƙo ta Hulɗa da Jama’a, Hakama Sidi Ali, ta fitar, ya ce rahoton ba gaskiya ba ne, ba a yaɗa gaskiyar yadda lamarin yake ba.

“Kuɗaɗen waɗanda adadin su ya kai Dala biliyan 1.259, waɗanda aka buga cikin jadawalin bayanan Adadin Musayar Kuɗaɗe na Watanni Ukun Farko na Shekarar 2025, suna nufin adadin kuɗaɗen da aka yi musaya a tsarin musayar kuɗaɗe na NFEM a fannoni daban-daban, har da fannin fetur da gas. Kuma a bisa cinikin da ya gudana can a tsakanin masu sayar da kuɗaɗe da masu saye, ba a CBN ba.”

Hakama ta ce tun bayan da aka haɗe tsarin musayar kuɗaɗen waje wuri ɗaya a ƙarƙashin NFEM cikin 2023, ‘yan kasuwa ne da kan su ke samo kuɗaɗen canji, ba CBN ke sayar masu ba.

Don haka ta ce “musamman ma batun sayar wa masu shigo da fetur Dalar Amurka, ko masu shigo kowane kaya, duk CBN bai sayar masu da Dala ba.”

Ta ce adadin wanda aka ci karo da shi a jadawalin, yana nufin adadin yawan Dalar da ‘yan kasuwa suka sayar wa masu sayen kuɗaɗen waje bisa tsarin da CBN ya gindaya, a cikin watanni ukun farkon watan Oktoba, 2025, wato Q1 2025.

Tags: CBNdaladillalaiHakama Sidi Ali
Previous Post

Tinubu ya yi afuwa ga wasu fursunoni, ya maida ofishin kwamitin afuwa zuwa Ma’aikatar Shari’a

Next Post

Farashin abinci yana ƙara sauƙi a yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Farashin abinci yana ƙara sauƙi a yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki

Farashin abinci yana ƙara sauƙi a yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!