Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a yau Litinin ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa.
An ga bidiyoyin magoya baya da masu adawa da El-Rufain sun bazu a soshiyal midiya yayin da ya je domin amsa gayyatar.
A halin da ake ciki kuma, hukumar DSS ta shigar da ƙara a kan El-Rufai kan zargin sa hannu a kutse da sauraren layukan wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu.
A cikin tuhuma uku mai lamba FHC/ABJ/CR/99/2026, wadda aka shigar a safiyar yau a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, jami’an tsaron sun zargi tsohon gwamnan da karya Dokar Hana Laifukan Yanar Gizo (Cybercrimes Prohibition Act, 2024) da kuma Dokar Sadarwa ta Nijeriya (Nigerian Communications Act, 2003).
Tuhumomin da ke cikin ƙarar sun ce:
“Cewa kai, Malam Nasir El-Rufai, baligi, namiji, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, yayin da ka fito a matsayin baƙo a shirin Prime Time na tashar talbijin ta Arise a Abuja, a cikin hurumin wannan kotu, ka amsa a yayin hirar cewa kai da wasu abokan hulɗar ka kun yi wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribaɗu, kutsen sauraren wayar sa ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan laifi ne da ya saɓa wa doka kuma ake hukunta shi ƙarƙashin Sashe na 12(1) na Dokar Hana Laifukan Yanar Gizo (Prohibition, Prevention, etc) ta 2024.
“Haka kuma, cewa kai, Malam Nasir El-Rufai, baligi, namiji, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, yayin da kake baƙo a shirin Prime Time na tashar talbijin ta Arise a Abuja, a cikin hurumin wannan kotu, ka bayyana cewa ka san kuma kana hulɗa da wani mutum da ya yi wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribaɗu, kutse da sauraren wayar sa ba bisa ƙa’ida ba, amma ba ka kai rahoton mutumin ga hukumomin tsaro da suka dace ba; wanda hakan laifi ne da ya saɓa wa doka kuma ake hukunta shi ƙarƙashin Sashe na 27(b) na Dokar Hana Laifukan Yanar Gizo (Prohibition, Prevention, etc) ta 2024.
“Haka kuma, cewa kai, Malam Nasir El-Rufai, baligi, namiji, tare da wasu da har yanzu ba a kama su ba, a wani lokaci cikin shekarar 2026 a Abuja, a cikin hurumin wannan kotu, kun yi amfani da kayan aiki ko tsarin fasaha da suka jefa tsaron jama’a da tsaron ƙasa cikin haɗari, tare da haddasa fargabar rashin tsaro a tsakanin ’yan Nijeriya, ta hanyar kutse da sauraren wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ba bisa ƙa’ida ba—abin da ka amsa a yayin wata hira a ranar 13 ga Fabrairu, 2026 a shirin Prime Time na tashar talbijin ta Arise a Abuja—wanda hakan laifi ne da ya saɓa wa doka kuma ake hukunta shi ƙarƙashin Sashe na 131(2) na Dokar Sadarwa ta Nijeriya ta 2003.”







