Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA) sun musanta zargin cewa sun sayi wani sinadari mai matuƙar guba, tare da umurtar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya miƙa duk wata shaida da yake da ita ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) domin gudanar da bincike.
Wannan lamari ya biyo bayan wata wasiƙa da El-Rufa’in ya aike wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, mai kwanan wata 30 ga Janairu, 2026, inda ya nemi ƙarin bayani kan abin da ya bayyana a matsayin zargin sayen kimanin kilo 10 na sinadarin thallium sulphate da ONSA suka yi.
A cikin wasiƙar tasa, El-Rufai ya ce an ruwaito cewa an samo sinadarin ne daga wani mai samar da kaya a ƙasar Poland, kuma ofishin NSA ne suka saye shi.
Ya kuma bayyana cewa ana zargin wasu shugabannin ‘yan adawa sun samu bayanai game da wannan sayayya.
An san thallium sulphate a matsayin sinadari mai tsananin guba, mara launi kuma mara ƙamshi, wanda kan iya haddasa mummunar illa ko da a ƙananan adadi.
Zargin ya haddasa damuwa a tsakanin jama’a tare da ƙara zafafa taƙaddamar siyasa tsakanin tsohon gwamnan da shugabannin tsaro na yanzu.
A cikin martanin da aka rubuta ranar 14 ga Fabrairu, 2026, wanda Birgediya Janar O.M. Adesuyi ya sanya wa hannu a madadin NSA, ONSA sun musanta zargin baki ɗaya.
Wasiƙar ta tabbatar da cewa sun karɓi wasiƙar El-Rufai a ranar 11 ga Fabrairu, 2026, tare da bayyana cewa Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro “bai taɓa sayen wannan sinadari ba, kuma bai fara bin wata hanya ta sayen sa ba, kuma ba shi da niyyar yin hakan.”
Har ila yau, martanin ya nuna cewa an miƙa zargin ga DSS domin gudanar da cikakken bincike.
A cewar wasiƙar, DSS za su gayyaci El-Rufai da duk wasu ɓangarori da ka iya mallakar bayanai masu alaƙa da zargin domin su gabatar da shaidu da za su taimaka wajen tabbatar da gaskiya.
“Mai Girma da sauran ɓangarorin da abin ya shafa, waɗanda ka iya mallakar bayanai masu alaƙa da wannan zargi, za a gayyace su yadda ya kamata domin su gabatar da duk wata shaida da za ta taimaka wajen gudanar da cikakken bincike da tabbatar da gaskiya,” inji wasiƙar.
Miƙa lamarin ga DSS na nuna niyyar Gwamnatin Tarayya ta barin hukumomin tsaro su gudanar da bincike a hukumance.
Majiyoyin da suka san abin da ya faru sun ce an fuskanci ƙalubale a yunƙurin isar da wasiƙar martanin ga El-Rufai a gidan sa da ke Abuja.
An ruwaito cewa masu gadi sun ƙi karɓar wasiƙar a ranar Juma’a, suka sanar da ɗan aiken cewa shugaban su ba ya nan, kuma ba su san lokacin da tsohon gwamnan zai kasance a gida ba.
Sai dai daga bisani an samu nasarar isar da wasiƙar a yau Lahadi, inda shugaban tsaron ya sanya hannu a takardar tare da karɓar ta a madadin El-Rufai.
Wannan musayar wasiƙu ita ce ta baya-bayan nan a cikin jerin saɓanin ra’ayi a fili da ke wanzuwa tsakanin El-Rufai da hukumomin Gwamnatin Tarayya.







