• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Doka ta bada damar hukunta masu wulaƙanta takardun Naira, inji CBN wurin taron wayar da kai a Inugu

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 18, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Doka ta bada damar hukunta masu wulaƙanta takardun Naira, inji CBN wurin taron wayar da kai a Inugu
Riƙe takardun naira

Riƙe takardun naira

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi kakkausan gargaɗi cewa dokar ƙasa ta tanadi hukunci kan masu wulaƙanta takardun Naira.

Gargaɗin ya fito ne daga bakin Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a, Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Hakama Sidi Ali.

Ta yi wannan gargaɗi a wurin taron gangamin wayar da kai da CBN ya shirya, ranar Talata, a Inugu.

Ta ce duk wani nau’in wulaƙanta takardun Naira, akwai dokar da ta tanadi hukunci a kan sa. Saboda haka ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su riƙe tare da tu’ammali da takardun Naira cikin daraja da tsafta.

“Lallai muna jaddada kira da babbar murya ga ‘yan Nijeriya cewa: su daina watsi da Naira ko liƙi a wurin bukukuwa, su daina sayar da takardun Naira, a guji duƙunƙune Naira, sa mata datti da kauce wa kuɗin jabu. Saboda darajar takardar Naira darajar ƙasar mu ce.”

Ta ce riƙe takardun Naira ana hadahada da su a cikin daraja da tsafta, abu ne mai muhimmanci wajen inganta harkokin kuɗaɗe na yau da kullum, kuma hakan na ƙarfafa tsarin saye da sayarwa tsakanin mai biyan kuɗi da mai sayarwa.

Hakama ta kuma shawarci jama’a su riƙa dagaro da hanyoyin da CBN ya tanadar domin samun sahihan bayanan da suka shafi CBN, musamman kan abin da ya shafi tsare-tsare, ƙa’idoji da sharuɗɗan da CBN ke gindayawa.

Ta ce tsare-tsaren inganta tattalin arziki irin su saisaita tsarin musayar kuɗaɗen waje zuba na bai-ɗaya, sa-ido wajen yin aiki filla ba tare da nuƙu-nuƙu ba, hakan ya ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗaɗe, ya bunƙasa asusun kuɗaɗen waje, kuma yana kan kankaro wa Naira darajar ta a kasuwar musayar kuɗaɗe.

Daraktar ta ƙara da cewa a ƙarƙashin Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, an ɗauki ƙwararan matakai ɗora tattalin arziki kan miƙaƙƙar hanya, cikin matakan da ta ce an ɗauka har da ƙarfafa jarin bankuna da sauran su.

A wurin taron dai an bai wa masu ruwa da tsaki da sauran jama’a damar yin tambayoyi, ana kuma ba su amsa kan abubuwan da suka shige masu duhu dangane da tsare-tsaren CBN.

Tags: CBNHakama Sidi AliNairawayar da kai
Previous Post

CBN ya tashi haiƙan: Malejin farashin kayayyaki ya ƙara yin ƙasa zuwa kashi 16.05, yayin da asusun kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 46.7

Next Post

Tinubu ya tura Shettima zuwa Kebbi don jaje kan sace ‘yan sakandare mata

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Tinubu ya rattaba hannu a dokar kafa cibiyoyin horas da ‘yan sanda

Tinubu ya tura Shettima zuwa Kebbi don jaje kan sace 'yan sakandare mata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!