• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Dalilin da ya sa na yi murabus daga Hukumar Alhazai – Farfesa Usman

ALI KANO by ALI KANO
February 10, 2026
in Labarai
A A
0
Dalilin da ya sa na yi murabus daga Hukumar Alhazai – Farfesa Usman
Farfesa Abdullahi Saleh Usman

Farfesa Abdullahi Saleh Usman

Tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce murabus ɗin da ya yi daga hukumar ya samo asali ne daga dalilai a na ƙashin kan sa, bayan yin addu’a da tuntuɓar ‘yan’uwan sa.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kan sa domin sanar da murabus ɗin a hukumance, ya bayyana cewa ya miƙa takardar murabus ɗin sa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce: “Ina so in bayyana ƙarara cewa na ɗauki wannan mataki ne gaba ɗaya saboda dalilai na ƙashin kai. Bayan yin addu’a da nazari mai zurfi tare da tuntuɓar iyali na, na yanke wannan shawara cikin lamiri mai tsafta da kuma girmamawa ga alhakin hidimar jama’a mai tsarki.

“Cikin zurfin tunani da godiya ga Allah SWT, ina sanar da murabus ɗi na daga muƙamin Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Nijeriya, wanda zai fara aiki daga Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.

“Dangane da tanade-tanaden Dokar NAHCON Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Nijeriya ta shekarar 2006, na miƙa murabus ɗi na a rubuce ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu (GCFR).”

Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da karramawar da ya yi masa ta naɗa shi domin yi wa Nijeriya da al’ummar Musulmi hidima a wannan matsayi.

“Amincewar da ka nuna a gare ni wata gata ce da zan riƙa alfahari da ita har abada. Ina kuma miƙa godiya ta ga Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, bisa jagoranci, ƙarfafawa da goyon bayan da ya ba ni a tsawon lokacin da na yi a wannan muƙami.

“Ga mambobin Hukumar, ina miƙa godiya ta ta gaske. Ga jami’an gudanarwa da ma’aikatan Hukumar, na gode da haɗin kai, jajircewa da kuma ruhin aiki tare da kuka nuna. Ƙwarewar ku, juriyar ku da tsayuwar ku kan hidima sun kasance abin koyi.

“Haka kuma ina miƙa godiya ta ga abokan hulɗar mu – Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kamfanonin yawon buɗe ido, kamfanonin jiragen sama da masu samar da ayyuka, da kuma takwarorin mu a Masarautar Saudiyya – waɗanda haɗin gwiwar su ya inganta ayyukan Hajjin Nijeriya sosai.”

Ya ƙara jaddada cewa murabus ɗin nasa ya samo asali ne kawai daga dalilai na ƙashin kai, kuma ba ya nuna wata rashin jin daɗi da Hukumar ko gwamnati ko kuma muhimmin aikin da suke aiwatarwa tare.

Ya ce: “Yayin da nake sauka daga wannan muƙami, addu’o’i na na tare da ku baki ɗaya. Ina roƙon Allah (SWT) cikin rahamar sa marar iyaka Ya karɓi ɗan ƙoƙarin mu, Ya shiryar da Ya albarkaci Shugaban Ƙasa da sabon shugabancin NAHCON, kuma Ya ba dukkan alhazai masu zuwa Hajji abin karɓaɓɓe (Hajj Mabrur).”

Tags: alhazaiFarfesaAbdullahiSalehUsmanHajji2026NAHCON
Previous Post

Taron NEC na 2026: Gwamnan CBN ya yi gargaɗin barazanar yawan kuɗi da guguwar zaɓen 2027 kan nasarorin tattalin arziki da aka sha wahalar samu

Next Post

Tinubu ya naɗa Magaji Da’u Aliyu a matsayin shugaban cibiyar binciken nukiliya ta ƙasa, ya kuma sabunta shugabancin NEMSA

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Tinubu ya naɗa Magaji Da’u Aliyu a matsayin shugaban cibiyar binciken nukiliya ta ƙasa, ya kuma sabunta shugabancin NEMSA

Tinubu ya naɗa Magaji Da’u Aliyu a matsayin shugaban cibiyar binciken nukiliya ta ƙasa, ya kuma sabunta shugabancin NEMSA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!