• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Limamin Abuja ya yi Allah-sambarka da mulkin Tinubu yayin da Matawalle ya aurar da ‘ya’ya goma

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 6, 2026
in Labarai
A A
0
Limamin Abuja ya yi Allah-sambarka da mulkin Tinubu yayin da Matawalle ya aurar da ‘ya’ya goma
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana musabaha da Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Bello Matawalle, a wajen ɗaurin auren a Masallacin Ƙasa da ke Abuja a yau Juma'a 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana musabaha da Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Bello Matawalle, a wajen ɗaurin auren a Masallacin Ƙasa da ke Abuja a yau Juma'a 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana musabaha da Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Bello Matawalle, a wajen ɗaurin auren a Masallacin Ƙasa da ke Abuja a yau Juma’a

Limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Luqman Zakariyah, ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu’ar fatan alheri, yana mai cewa mulkin sa zai dawo da kyakkyawar fata a cikin al’umma.

Zakariyah ya yi addu’ar ne a yau Juma’a a Masallacin Ƙasa a lokacin da Tinubu ya halarci ɗaurin auren auren ’ya’yan Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Bello Matawalle, inda ya wakilci ‘ya’yan Matawalle a matsayin uba ga amaren da angunan.

Ana ɗaura aurarrakin

Limamin ya ce, “Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya ba Shugaban Ƙasar mu, wanda ke wakiltar kowa, lafiya da tsawon rai, ya kuma ba shi nasara da albarka a shugabancin sa. Muna addu’ar mulkin sa ya zama abin kyakkyawar fata ga ‘yan ƙasa.”

Matawalle, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, ya aurar da ’ya’yan sa mata guda biyar, Maryam, Safiyya, Farida, Nana Firdausi da A’isha, yayin da ’ya’yan sa maza guda biyar, Ibrahim, Abdul Jalal, Surajo, Bello da Fahad, su ma suka yi aure.

Shugaba Ƙasa ya zama waliyyin amaren a madadin iyalan Matawalle, inda limamin ya kuma yi addu’ar Allah ya albarkaci auren, ya ba ma’auratan zaman lafiya da nasara a rayuwar su.

Shugaban Ƙasar São Tomé and Príncipe, Carlos Manuel Vila Nova, yana daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron.

Gwamnonin jihohi, ’yan Majalisar Tarayya, membobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya, manyan hafsoshin tsaro, jami’an diflomasiyya, sarakunan gargajiya, malamai da sauran al’umma duk sun halarci ɗaurin auren.

Tinubu yana gaisawa da Shugaban Ƙasar São Tomé and Príncipe, Carlos Manuel Vila Nova, a Masallacin Ƙasa
Tags: BelloMohammedMatawalledaurinaureLimaminAbujaMasallacinƘasaShugabaBolaTinubu
Previous Post

Sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu suna daidaita Nijeriya — Idris

Next Post

Cika shekaru 50: Hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin Janar Murtala ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa bisa aƙidun sa – Gwamnan Legas

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Cika shekaru 50: Hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin Janar Murtala ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa bisa aƙidun sa – Gwamnan Legas

Cika shekaru 50: Hanya mafi ma’ana ta girmama tarihin Janar Murtala ita ce ci gaba da aiki domin gina ƙasa bisa aƙidun sa - Gwamnan Legas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!