• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya yi farin cikin cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 26, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa cire sunan Nijeriya daga ƙasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su a duniya cewa, hakan tabbaci ne da ke nuna duniya ta gamsu da tsare-tsaren tattalin arzikin da wannan gwamnati ta bijiro da su.

Cikin wata sanarwar da Daraktar Riƙon Sashen Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai, Hakama Sidi Ali, ta sa wa hannu kuma ta fitar a ranar Asabar, ta nuna cewa duniya ta gamsu da tsare-tsaren harkokin kuɗaɗe da kuma gagarumin yaƙi da almundahanaha da zambar kuɗaɗen da ake kan yi a Nijeriya.

CBN ya ci gaba da cewa an cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke sa-ido kan su, bayan kwamitin sa-ido ɗin ya gani tare da tabbatarwa irin “gagarumin cigaban” da Nijeriya ta samu wajen yi wa tsare-tsaren kuɗaɗe ragama da linzamin daƙile zambar kuɗaɗe da kuma datse hanyoyin safarar kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.

FATF dai ƙaƙƙarfar hukumar sa-ido ce ta duniya wadda ke lura kan hada-hada da harƙallar kuɗaɗe ta ɓarauniyar hanya. Ta bayyana cire sunan Nijeriya a ranar Juma’a, tare da ƙasashen Afrika ta Kudu, Mozambik, Burkina Faso.

Hakama Ali ta ci gaba da cewa cire sunan Nijeriya ya nuna irin kyakkyawan tasirin da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da CBN, Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Lura da Hada-hadar Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) da kuma EFCC suka yi.

“Rawar da CBN ya taka wajen samun wannan nasara ta shafi tabbatar da sa-ido sosai, tsara ƙa’idoji, gindaya sharuɗɗ da gudanar da ayyuka ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen hada-hadar kuɗaɗe.”

Daga cikin tsare-tsaren da FATF tare da Kafofin Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe na Afrika ta Yamma su ka yi wa bin diddigi, akwai tsarin lambobin sirrin bibiyar Tsarin Musayar Kuɗaɗe, wadda aka ƙirƙiro domin rage harƙalla a hada-hadar musayar kuɗaɗe.

Cire Nijeriya daga ƙasashen da ake kaffa-kaffa da su ɗin zai ƙara cire shakku kan Nijeriya, tare da faɗaɗa hada-hadar cinikayya tsakanin ƙasar da ƙasashen waje, cibiyoyi da masu zuba jari. Haka bankuna za su samu ƙarin hulɗoɗi da masu son haɗin gwiwa daga waje.

An dai saka sunan Nijeriya cikin ƙasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffa da su a cikin 2021, bayan duniya ta nuna rashin amincewa dangane da yadda salon yaƙi da zambar kuɗaɗe ke gudana, musamman wajen matsalar yadda ake samun safarar muggan kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.

Tags: CBNHakama Sidi Ali
Previous Post

Ƙungiyar NFTD ta jinjina wa Yakubu, Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya

Next Post

Nijeriya za ta karɓi baƙuncin gudanar da taron farko na IPI Afrika

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Nijeriya za ta karɓi baƙuncin gudanar da taron farko na IPI Afrika

Nijeriya za ta karɓi baƙuncin gudanar da taron farko na IPI Afrika

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!