Kaftin Yosef-Haim Ashraf ya zama sojan Isra’ila na 18 da ya kashe kan sa saboda da-na-sanin kisan Falasɗinawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu ta tura shi ya yi a yankin Gaza.
A manyan biranen Isra’ila dai ana ci gaba da zanga-zangar rashin goyon bayan ci gaba da yaƙin yunƙurin mamaye yankunan Gaza da Netanyahu ya ƙudiri yi.
Da yawan wasu masu zanga-zanga ɗin kuma suna yi ne da nufin a tsaida yaƙi domin a sulhunta, ta yadda ƙungiyar kare Falasɗinawa ta Hamas za ta saki ‘yan’uwan su Yahudawa da ke tsare a hannun su.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu manyan ƙasashe a Turai ke shelar amincewa da Falasɗinu matsayin ƙasa mai cin gashin kai, da suka ce za su ayyana a cikin Satumba.





