Ƙungiyar Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda ta rantsar da shugabannin ta na Jihar Neja da masu tsara ayyukan ta ƙananan hukumomi 25 na jihar, tare da kira ga mambobin ta da su mayar da manufofin ƙungiyar zuwa ayyukan da za su amfani al’umma.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a Cibiyar Mata da ke Minna, babban birnin jihar Neja, inda masu ruwa da tsaki suka jaddada muhimmancin ƙarfafa mata, bunƙasa kasuwancin su, faɗaɗa shigar su harkokin siyasa da inganta haɗin kai wajen cimma manufofin ƙungiyar.
Mai tsara ayyukan ƙungiyar a jihar Neja, Mary Noel Barje, ta bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne domin ƙarfafa rawar da mata ke takawa a harkokin siyasa, tare da tallafa musu wajen bunƙasa kasuwanci da shiga sauran fannoni na cigaba.
Ta kuma buƙaci mambobin ƙungiyar da su zama jakadu nagari, ta hanyar gudanar da ayyukan su bisa gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa manufofin ƙungiyar sun amfani al’umma.
A jawaban su daban-daban, Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Ayyukan Ban Ruwa, Faruq Umar Audi, da Hadiza Sharu, wadda ta wakilci Kwamishinar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma, sun buƙaci sababbin shugabannin da aka rantsar da su da su gudanar da ayyukan su bisa gaskiya, riƙon amana da kishin al’umma.
Sun kuma jaddada muhimmancin kare muradun mata, inganta walwalar su da samar da damarmaki da za su ba su damar taka rawar gani a cigaban jihar.
Sauran waɗanda suka gabatar da jawabai, ciki har da wasu daga cikin sababbin shugabannin, sun yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin kai da aiki tare, tare da faɗaɗa shigar mata a harkokin siyasa da sauran ayyukan ci gaban al’umma.
A yayin bikin, shugabannin ƙungiyar guda 15 sun yi rantsuwar kama aiki a gaban Alkaliya kuma Daraktar Harkokin Dokar Kare Haƙƙin Yara, Barista Ummu-Kattum Muhammad.







