• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Ƙungiyar ‘Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda’ ta rantsar da shugabannin ta na Neja

WAKILIN MU by WAKILIN MU
October 29, 2026
in Siyasa
A A
0
Ƙungiyar ‘Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda’ ta rantsar da shugabannin ta na Neja
Mambobin ƙungiyar 'Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda' a wurin taron rantsar da shugabannin ta na Jihar Neja da masu tsara ayyukan ta  na ƙananan hukumomi 25 na jihar, a Cibiyar Mata da ke Minna, babban birnin jihar

Mambobin ƙungiyar 'Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda' a wurin taron rantsar da shugabannin ta na Jihar Neja da masu tsara ayyukan ta  na ƙananan hukumomi 25 na jihar, a Cibiyar Mata da ke Minna, babban birnin jihar

Ƙungiyar Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda ta rantsar da shugabannin ta na Jihar Neja da masu tsara ayyukan ta  ƙananan hukumomi 25 na jihar, tare da kira ga mambobin ta da su mayar da manufofin ƙungiyar zuwa ayyukan da za su amfani al’umma.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a Cibiyar Mata da ke Minna, babban birnin jihar Neja, inda masu ruwa da tsaki suka jaddada muhimmancin ƙarfafa mata, bunƙasa kasuwancin su, faɗaɗa shigar su harkokin siyasa da inganta haɗin kai wajen cimma manufofin ƙungiyar.

Mai tsara ayyukan ƙungiyar a jihar Neja, Mary Noel Barje, ta bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne domin ƙarfafa rawar da mata ke takawa a harkokin siyasa, tare da tallafa musu wajen bunƙasa kasuwanci da shiga sauran fannoni na cigaba.

Ta kuma buƙaci mambobin ƙungiyar da su zama jakadu nagari, ta hanyar gudanar da ayyukan su bisa gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa manufofin ƙungiyar sun amfani al’umma.

A jawaban su daban-daban, Kwamishinan Albarkatun Ruwa da Ayyukan Ban Ruwa, Faruq Umar Audi, da Hadiza Sharu, wadda ta wakilci Kwamishinar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma, sun buƙaci sababbin shugabannin da aka rantsar da su da su gudanar da ayyukan su bisa gaskiya, riƙon amana da kishin al’umma.

Sun kuma jaddada muhimmancin kare muradun mata, inganta walwalar su da samar da damarmaki da za su ba su damar taka rawar gani a cigaban jihar.

Sauran waɗanda suka gabatar da jawabai, ciki har da wasu daga cikin sababbin shugabannin, sun yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin kai da aiki tare, tare da faɗaɗa shigar mata a harkokin siyasa da sauran ayyukan ci gaban al’umma.

A yayin bikin, shugabannin ƙungiyar guda 15 sun yi rantsuwar kama aiki a gaban Alkaliya kuma Daraktar Harkokin Dokar Kare Haƙƙin Yara, Barista Ummu-Kattum Muhammad.

Tags: Business Women of Influence for Renewed Hope AgendaNejarantsarwasiyasazaben2027
Previous Post

Gwamnatin Tarayya za ta ba ma’aikata tallafin sufuri na N70,000 kowane wata

Next Post

Kashi 57 cikin 100 na cibiyoyin kuɗi ne suka shirya bin ƙa’idar adana bayanai a Nijeriya – CBN

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Yadda tawagar wayar da kai daga CBN ta baje koli a Gombe, ta dira Bauchi domin ƙara shigar da jama’a cikin harkokin kuɗi da inganta cigaban tattalin arziki

Kashi 57 cikin 100 na cibiyoyin kuɗi ne suka shirya bin ƙa’idar adana bayanai a Nijeriya - CBN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!