Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) sun bayyana cewa zuwa yanzu dai kashi 57 cikin 100 ne kaɗai na cibiyoyin kuɗi a Nijeriya suka shirya bin ƙa’idar adana bayanan mu’amalolin kuɗi a cikin Nijeriya.
Sai dai kuma hukumomin CBN da NITDA sun nuna kyakkyawan fata cewa sauran cibiyoyin za su kammala shirye-shiryen su kafin wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2027 ya cika.
Hukumomin biyu sun bayyana hakan ne a ranar Laraba, wurin taron tattaunawa tsakanin masu kula da harkokin kuɗi da fasahar sadarwa, mai taken ‘Executive Regulatory Dialogue on National Sovereign Cloud Initiative (NSCI) and Data Localisation Implementation’, wanda aka gudanar a Legas.
Taron ya samu halartar bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi (fintechs), masu samar da kayayyakin more rayuwa na biyan kuɗi da sauran masu ruwa da tsaki, domin tattauna matakan da ake buƙata wajen bin sabuwar ƙa’idar.
Yayin da ya rage ƙasa da watanni uku kafin wa’adin, CBN da NITDA sun ce sun fi mayar da hankali kan wayar da kai da bayar da jagoranci domin taimaka wa cibiyoyin da ba su kammala shirye-shiryen su ba. Sai dai sun yi gargaɗin cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa kan duk wata cibiya da ta ƙi bin ƙa’idar da gangan.
CBN Ya Bada Wa’adin 1 Ga Janairu, 2027:
A ranar 15 ga Yuni, 2026, CBN ya fitar da wata sanarwa mai ɗauke da sabbin ƙa’idoji kan adana bayanai a cikin gida, tsarin kasuwar biyan kuɗi, bayyana ainihin masu mallakar kamfanoni da kuma sa-ido kan tsarin biyan kuɗi a cikin Nijeriya.
Ƙa’idar ta tanadi cewa cibiyoyin da ke ƙarƙashin kulawar bankin dole ne su tabbatar da cewa ana adana muhimman bayanan hada-hadar kuɗi da aka samar a Nijeriya tare da sarrafa su a cikin ƙasar nan.
An tsara fara aiwatar da ƙa’idar ne daga ranar 1 ga Janairu, 2027.
CBN ya ce zai taimaka wa cibiyoyin da ba su shirya ba, a ta bakin Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Rakiya Yusuf, ta ce an shirya taron ne domin fayyace wa masu ruwa da tsaki abubuwan da ƙa’idar ta ƙunsa tare da taimaka masu su shirya yadda ya kamata kafin fara aiwatar da tsarin.
Rakiya ta ce wani binciken da aka gudanar kafin taron ya nuna cewa fiye da rabin cibiyoyin kuɗi sun riga sun shirya bin ƙa’idar.
Ta bayyana cewa tana da yakinin sauran cibiyoyin za su samu ci gaba idan aka ƙara fayyace musu abubuwan da ake buƙata.
A cewarta, “Na yi farin ciki matuƙa da sakamakon binciken da muka gudanar domin tattara bayanai ya nuna cewa fiye da kashi 50 cikin 100 na cibiyoyin da ke wannan fanni sun shirya bin ƙa’idar.
“Saboda haka, sauran waɗanda ba su kai wannan mataki ba za su iya inganta shirye-shiryen su ta hanyar ƙarin bayanai da jagorancin da aka bayar.”
Ta ce CBN na da kyakkyawan fata cewa dukkan cibiyoyin za su bi ƙa’idar kafin wa’adin Janairu 2027.
Ta jaddada cewa manufar ƙa’idar ta shafi kare ikon Nijeriya kan bayanan ta, tabbatar da samun cikakken bayani kan hada-hadar kuɗi da kuma kiyaye daidaito da kwanciyar hankali a tsarin kuɗin ƙasar nan.
“A ƙarshe, muna fatan cewa zuwa Janairu 2027, dukkan cibiyoyi za su kasance sun fara adana bayanan biyan kuɗi a cikin Nijeriya.”
Ta ci gaba da cewa wannan lamari ne da ya shafi ikon ƙasar mu, samun cikakken bayani, sa-ido kan bayanan hada-hadar kuɗi da kuma tabbatar da wanzuwar hadahadar tsarin kuɗi bisa ƙa’ida, wanda hakan yana daga cikin muhimman ayyukan CBN.”
Daga nan sai CBN ya yi gargaɗin hukunta masu ƙin bin ƙa’idar da gangan, inda Rakiya ta ci gaba da cewa, “dangane da matakan da za a ɗauka kan waɗanda ba su bi ƙa’idar ba, to CBN ba zai fara da hukunci ba, sai dai ya fi son taimaka wa cibiyoyin su fahimci ƙa’idar tare da bin umarnin da aka bayar.”
Ta ce, “Hukunci ba shi ne abin da za mu fara tunani a kai ba wajen tabbatar da bin ƙa’idar. Abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne mu taimaka wa kowa, mu jagorance su har sai sun fahimci abin da ake buƙata.”
Sai dai ta yi gargaɗin cewa za a ɗauki mataki kan cibiyoyin da suka yi ƙoƙarin kawo cikas ga aiwatar da ƙa’idar da gangan.
“Amma idan muka ga cewa akwai yunƙurin hana aiwatar da tsarin da gangan, to, tabbas za a ɗauki matakin hukunci. Za a hukunta waɗanda suka ƙi bin ƙa’idar,” inji ta.







