Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kama wata ’yar jarida mai shekaru 23, Farida Isiak, da kuma yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari da wata kotun Shari’a da ke Kawo, a Kaduna, ta yi, tana mai bayyana matakin a matsayin ramuwar gayya da kuma yunƙurin daƙile ‘yancin aikin jarida.
Farida, wadda ke aiki a gidan Rediyon Nagarta da ke Kaduna, ta shiga hannun ’yan sanda ne a daren ranar Litinin, 20 ga Oktoba, bayan ta wallafa wani saƙo a Facebook inda ta soki ’yan sanda kan zargin mu’amala ba bisa ƙa’ida ba da suka yi wa iyayen ta.
A cikin wata sanarwa, Amnesty International Nigeria ta ce jami’an ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin jami’in da ke kula da ofishin ’yan sanda, wato Difi’o, na Mararaban Jos, Usman Adamu, sun kama ’yar jaridar da misalin ƙarfe 10 na dare.
A cewar ƙungiyar, lamarin ya samo asali ne daga saɓani tsakanin mahaifiyar Farida da wata maƙwabciyar su kan kuɗin canji na naira 100 da ya shafi cinikin gawayi.
Amnesty ta yi zargin cewa ’yan sanda sun fara kama mahaifiyar ’yar jaridar, sannan suka tsare mahaifin ta lokacin da ya je neman a sako matar sa. Ƙungiyar ta ce jami’an sun yi amfani da tsare iyayen ne domin tilasta wa Farida zuwa ofishin ’yan sanda.
Ta ce bayan Farida ta isa ofishin, jami’an ’yan sanda sun zarge ta da ɓata musu suna ta hanyar saƙon da ta wallafa a Facebook.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa duk da yake Farida ta bi umarnin jami’an na goge saƙon tare da ba da haƙuri, da fatan za a saki iyayen ta, sai kuma jami’an suka ci gaba da tsare ta, daga bisani suka gurfanar da ita a gaban wata kotun Shari’a da ke Kawo.
Rahoton ya ce kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari ko kuma biyan tarar naira miliyan 1.75 bisa zargin ɓata suna.
Amnesty International ta bayyana shari’ar a matsayin wadda ba a gudanar da ita yadda ya kamata ba, tana mai zargin cewa kotun ta yi watsi da yanayin da ya haddasa lamarin da kuma zargin rashin ɗa’a da jami’an ‘yan sanda suka yi.
Ƙungiyar ta ce kama Farida Isiak da yanke mata hukunci ya nuna cin zarafin iko da kuma amfani da tsarin shari’a wajen danne ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma tsoratar da ’yan jarida.
“Buƙatar a yi wa jami’an ’yan sanda hisabi kan ayyukan su haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya tanada,” inji ƙungiyar, tana mai cewa tsare iyayen ’yar jarida domin tilasta mata miƙa kan ta ga ’yan sanda wata dabara ce da ta saɓa wa doka da kuma tsarin mulkin ƙasa.
Amnesty ta yi kira ga rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna da hukumomin shari’a na Nijeriya da su tabbatar da sakin Farida ba tare da ɓata lokaci ba, su janye tuhume-tuhumen da ake yi mata, tare da soke tarar da aka yanke mata.
Haka kuma, ta buƙaci rundunar ’yan sandan Nijeriya da ta gudanar da cikakken bincike mai zaman kan sa kan yadda jami’an da abin ya shafa suka tsare iyayen ’yar jaridar bisa zargin da aka yi.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumomin Nijeriya da su daina amfani da tuhume-tuhumen ɓata suna da tsarin shari’a wajen cin zarafin ’yan jarida da kuma tauye ’yancin aikin jarida.
Hukumar ‘yan sanda dai ba su ba da wata sanarwa ba kan hukuncin har zuwa wannan lokacin.







