Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce gwamnatin sa za ta samar wa Malam Ahmed Abubakar Zakka da matar sa, Nafisah, da ’yar su Fatima, gida tare da ɗaukar nauyin dukkan kuɗaɗen jinyar su da kuma ba su kulawar lafiyar ƙwaƙwalwa da tunani.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da ya kai wa iyalan a gidan da gwamnatin jihar ta ware domin ba su mafaka a Kaduna, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci bayan an sallame su daga asibiti sakamakon kubutar da suka yi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 20 ga Oktoba, 2026, Uba Sani ya ce ya ji daɗin ganin daga yadda lafiyar iyalan ke inganta, yana mai fatan za su samu cikakkiyar lafiya.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa iyalan har bayan ziyarar, domin taimaka musu su murmure, su sake gina rayuwar su, tare da dawo musu da kwanciyar hankali da jin cewa suna cikin aminci.
Gwamnan ya bayyana cewa halin da iyalan suka shiga ya sake tunatar da jama’a irin illar rashin tsaro ga rayuwar al’umma da kuma babban nauyin da ke kan gwamnati na kare rayuka da dawo da zaman lafiya a kowane yanki.
Ya ƙara da cewa kuɓutar iyalan ta ƙara wa gwamnatin sa ƙwarin gwiwar ci gaba da yaƙi da ’yan fashi da makami da sauran masu aikata laifuka, ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, inganta tsarin gudanar da ayyukan tsaro da kuma kusantar al’umma.
Uba Sani ya jaddada cewa kowane mazaunin jihar yana da haƙƙin rayuwa ba tare da fargaba ba, yana mai cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da wannan haƙƙi.
Haka kuma, gwamnan ya nuna godiyar sa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa yadda ya shiga cikin lamarin da kuma nuna damuwa kan tsaron iyalan.
Ya kuma yaba wa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, da sauran hukumomin tsaro bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da dawowar iyalan cikin aminci.
Sanata Uba Sani ya ce Malam Ahmed Abubakar Zakka ya nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna da kuma hukumomin tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi da kuma kulawar da suke ba iyalan sa.
Ya ce jin daɗin da Ahmed ya nuna kan kulawar da yake samu, tare da amincewar sa cewa zai warke, abin jin daɗi ne yayin da gwamnati ke ci gaba da kasancewa tare da iyalan a wannan lokaci na murmurewa.
Gwamnan ya tabbatar da cewa jin daɗin iyalan da samun cikakkiyar lafiyar su za su ci gaba da kasancewa cikin muhimman abubuwan da gwamnatin sa za ta ba fifiko a watanni masu zuwa.






