Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Olayemi Cardoso, ya ce ba ya tilasta bin ra’ayin sa ga mambobin Kwamitin Kula da Manufofin Kuɗi (MPC), yana mai jaddada cewa ana la’akari da ra’ayoyin dukkan mambobin kwamitin wajen yanke shawara.
Cardoso ya bayyana cewa kasancewar mambobi biyar cikin kwamitin waɗanda ba a cikin bankin suke ba, hakan na taimakawa wajen rage yiwuwar bin ra’ayi guda ba tare da yin nazari mai zaman kan sa ba.
Gwamnan, wanda shi ne Shugaban Kwamitin MPC mai mambobi 12 da ke yanke shawarar ƙima da adadin kuɗin ladar karɓar ramce a bankuna a ƙasar nan, ya ce babban aikin sa shi ne jagorantar tattaunawa da tabbatar da cewa kowane mamba ya samu damar bayyana ra’ayin sa a cikin ƙwarewar da fahimtar sa.
Ya ce CBN na ƙoƙarin gina tsarin MPC da zai bai wa ra’ayoyin dukkan mambobin sa muhimmanci, ciki har da waɗanda ba sa cikin ma’aikatan bankin, domin tabbatar da inganci da sahihancin shawarwarin da ake yankewa.
A cewar Cardoso, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da bankin ke yi na ƙarfafa tsarin tsara manufofin kuɗi da kuma tabbatar da cewa ana yanke shawara bisa la’akari da ra’ayoyi daban-daban.
Kwamitin MPC ya ƙunshi mambobi bakwai daga cikin jami’an CBN da kuma mambobi biyar daga wajen CBN.
Cardoso ya ce shigar waɗannan mambobi na waje sun ƙara wa tsarin yanke shawara zurfi da sahihanci.
Gwamnan na CBN ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa mai taken “Yadda Manyan Bankuna Ke Yanke Shawara”, wanda aka gudanar a matsayin wani ɓangare na taron shekara-shekara na Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a birnin Bangkok na ƙasar Thailand, wanda aka kammala baya-bayan nan.







