Jami’an tsaro sun kama ɗan takarar neman kujerar Sanata mai wakiltar Taraba ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Alhaji Bello Boɗejo, a daren jiya Alhamis a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Boɗejo, wanda shi ne shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore, ya je Jalingo tun da farko a cikin jirgin sama mai zaman kan sa ta filin jirgin sama na Ɗanbaba Suntai da misalin ƙarfe 1:20 na rana.
Dubban magoya bayan sa daga ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa yankin sanatocin Taraba ta Tsakiya sun tarbe shi.
Da yake magana da Daily Trust ta wayar tarho, mataimakin sa na musamman, Umar, ya ce an kama ɗan takarar APC ɗin ne bayan ya kai ziyara wasu ofisoshin hukumomin tsaro tare da wasu na kusa da shi a siyasa.
A cewar sa, an kama shi ne a ɗaya daga cikin ofisoshin tsaron jim kaɗan bayan ya yi jawabi ga magoya bayan sa a sakatariyar APC ta jihar da ke Jalingo.
Umar ya ce an umurci mutanen da suka raka shi da su fice nan take, yayin da aka tsare Boɗejo.
“A halin yanzu, ba mu san inda aka kai shi ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Jami’an tsaron da suka raka shi tare da ba shi kariya daga Abuja zuwa Jalingo su ne daga baya suka kama shi.
“Har yanzu ba a sanar da mu dalilin kama shi ba, kuma babbar damuwar mu yanzu ita c e ba mu san inda ake tsare da shi ba.”
Kafin a kama shi, Boɗejo ya shaida wa ’yan jarida a sakatariyar APC cewa ya sayi fom ɗin tsayawa takarar sanata kuma ba zai janye wa kowane ɗan takara ba.
Ya jaddada cewa yana nan daram a takarar kuma ba zai miƙa wuya ga matsin lambar da ake masa na janye takarar sa ba.
“Na shiga wannan takara ne domin in yi nasara, kuma babu wanda zai tilasta mini na janye,” inji shi.
Har ila yau, ɗan takarar ya bayyana cewa kwamitin maslaha da ake cewa Gwamna Agbu Kefas ya kafa domin tattaunawa da ’yan takara a yankunan sanatoci uku na jihar bai tuntuɓe shi ba.
“Kwamitin maslahar da gwamnan ya kafa bai tuntuɓe ni ba, kuma ina so in bayyana a sarari cewa ba zan janye wa kowa ba, ko da kuwa akwai matsin lamba,” inji Boɗejo.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka kama shi ba.
A 2024, jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun taɓa kama shi bisa zargin kafa ƙungiyar sintiri a Jihar Nasarawa.
An kama shi a hedikwatar Miyetti Allah Kautal Hore da ke Kasuwar Shanu ta Tudun Maliya, Kilomita 22, kan hanyar Abuja zuwa Keffi, Tudun Wada, Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
An ce jami’an DSS tare da wasu sojojin rundunar sojin Nijeriya sun mamaye hedikwatar Miyetti Allah da misalin ƙarfe 3:40 na yamma, sannan suka tafi da shi bayan sun kama shi a ƙofar shiga.
Har yanzu ba a san ko wannan sabon kamen yana da alaƙa da siyasa ko kuma batun tsaro ba.







