Tsohuwar ‘yar takarar gwamna a Jihar Adamawa, Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, a yau Juma’a ta ba da sanarwar shiga jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), wanda ke nuna sabon matakin siyasa da take ɗauka gabanin zaɓen 2027.
Sauya sheƙar nata ya zo ne watanni tara bayan ta fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC.
Da take jawabi jim kaɗan bayan karɓar katin memba a NDC, Binani ta danganta matakin da ta ɗauka da abin da ta kira ƙudirin jam’iyyar na shugabanci mai tsari da kuma tasirin mabiyan ta.
Ta ce: “Na san da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya na tambayar dalilin da ya sa na yanke shawarar shiga NDC. Amsar mai sauƙi ce. Bayan na yi nazari sosai kan kundin tsarin jam’iyyar, na ga akwai ƙwarin gwiwa mai ƙarfi na shugabanci mai tsari da kuma tafiyar da manufofi bisa tsari.
“Wasu za su iya cewa watanni tara kacal da suka wuce ina wata jam’iyya. Ina so in bayyana cewa ba zan taɓa zagin inda na fito ba. Siyasa tana sauyawa, kuma sau da yawa tana da alaƙa da yanayin wuri, kuma ana yanke shawara bisa ga halin da ake ciki.
“Amma abin da na fi bai wa muhimmanci shi ne muradun mabiya na. Kimanin watanni tara da suka wuce, mun yanke shawarar shiga tsohuwar jam’iyyar mu tare. Amma daga baya, bisa dalilai da suka sani, mabiya na sun ga ya dace mu ci gaba da tafiya gaba. Su ne suka fara kuma suka buƙaci in shiga NDC.”
Ta ƙara da cewa matakin shiga NDC ya samo asali ne daga mabiyan ta, waɗanda tuni suka fara samun tasiri a cikin jam’iyyar kafin ita ta shiga a hukumance.
Ta jaddada muhimmancin mabiyan ta a tafiyar ta ta siyasa, tana mai bayyana su a matsayin ginshiƙin nasarorin ta, tare da nuna godiya ga amincin su.
Ta ce: “Tun ma kafin in yanke hukunci na ƙarshe, sun riga sun yi nisa a cikin jam’iyyar. A yau, Jihar Adamawa tana daga cikin jihohin da ke da mafi yawan membobin NDC. A ko yaushe nakan ce babu wanda zai yi nasara shi kaɗai a siyasa. Magoua baya ne ke jan ragamar tafiya, su ne ke gina tushe, kuma su ne ke ci gaba da ɗorewa da tafiyar.
“Duk abin da na samu a siyasa ya samo asali ne daga ƙaƙƙarfan goyon bayan su, kuma ina matuƙar godiya. A wannan lokaci, ina so in gode wa Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na NDC saboda karɓar mu hannu biyu-biyu da suka yi.
“Abin da muke nema shi ne adalci, daidaito, gaskiya, riƙon amana, da kuma ƙarfafa dimokiraɗiyyar cikin gida. Waɗannan su ne ginshiƙan nasarar jam’iyya na dogon lokaci.”
Yayin da yake maraba da Binani da mabiyan ta, jagoran NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana jam’iyyar a matsayin wadda ke karɓar kowa kuma a shirye take ta faɗaɗa ƙarfin ta.
Ya ce: “Ƙofar wannan jam’iyya a buɗe take, mai karɓar kowa, kuma a shirye take ta haɗa ƙarfin ku, ra’ayoyin ku da gudunmawar ku. ‘Yar’uwa ta, barka da zuwa. Kamar yadda shugaban ya faɗa, tutar jagorancin NDC a Adamawa yanzu tana hannun ki.
“Muna da yaƙinin cewa bayan kammala tsarin dimokiraɗiyyar jam’iyyar, za mu sake haɗuwa a Adamawa domin ci gaba da gina wannan tafiya tare da al’ummar jihar.”
Ya buƙaci ‘yan siyasa da ba su gamsu da jam’iyyun su ba da su sake duba matsayin su, yana mai jaddada cewa babu wanda ya kamata ya ji kamar an tilasta masa zama a jam’iyyar da ba ta yi masa amfani.
Ya ce: “Ga waɗanda suka shiga wasu jam’iyyu kuma yanzu suna ganin yadda abubuwa suke, ina tunatar da ku—ba a makara ba. Kada ku bari a tsoratar da ku ko a ruɗe ku cewa ba za ku iya barin jam’iyya ba. Wannan ba shi ne dokar Nijeriya ba.
“Kowane ɗan Nijeriya yana da ‘yancin shiga kowace jam’iyya a kowane lokaci—kuma ya fita a kowane lokaci. Siyasa tafiya ce. Idan abin hawa da kuka hau ba ya kai ku inda kuke so, kuna da ‘yancin sauka ku hau mafi alheri.
“NDC ita ce wannan abin hawa mafi alheri—mai ƙarfi, abin dogaro, kuma mai mai da hankali kan sakamako.”
Sauya sheƙar Binani ya ƙara nuna yadda tafiyar ta ta siyasa take canzawa a ‘yan shekarun nan.
Tsohuwar ‘yar majalisar ta kasance ‘yar takarar gwamna ta APC a zaɓen Adamawa na 2023, inda ta fafata sosai da gwamna mai ci, Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP, a ɗaya daga cikin zaɓukan da suka fi ɗaukar hankali da jawo ce-ce-ku-ce.
A wani lokaci mai ɗaukar hankali yayin tattara sakamako, an ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara daga hannun Kwamishinan Zaɓe na Jihar, Hudu Yunusa Ari, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.
Daga bisani, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta soke wannan sanarwa tare da dakatar da kwamishinan.
Ana sa ran shigar ta NDC za ta sauya yanayin siyasa a Jihar Adamawa, yayin da jam’iyyu suke fara shirin tunkarar zaɓe na gaba.







